Sojoji sun sheke 'yan bindiga 4, sun samu miyagun makamai a Katsina

Sojoji sun sheke 'yan bindiga 4, sun samu miyagun makamai a Katsina

- Dakarun soji sun sheke 'yan bindiga 4 a yayin wata arangama da suka yi a kauyen Marina

- Tun farko sojojin sun hango 'yan bindigan dauke da shanun sata a karamar hukumar Safana

- An samo miyagun makamai da babur daga sauran 'yan bindigan kafin su tsere da raunika

Zakakuran sojin Najeriya sun sheke wasu mutum hudu da ake zargin 'yan bindiga ne karkashin rundunar Operation Hadarin Daji a Katsina, The Cable ta wallafa.

Sojojin sun yi musayar wuta da 'yan bindigan a ranar Alhamis a kauyen Marina dake karamar hukumar Safana ta jihar.

Akasin rahotannin da ke yawo na cewa an halaka sojoji masu yawa a yankin, Mohammed Yerima, kakakin rundunar sojin a wata takarda da ya fitar a ranar Asabar, yace soja daya ne ya rasa rayuwarsa a yayin musayar wutar.

KU KARANTA: Tsohuwar matar Fani-Kayode ta maka shi gaban kotu, tana son karbar 'ya'yansu

Sojoji sun sheke 'yan bindiga 4, sun samu miyagun makamai a Katsina
Sojoji sun sheke 'yan bindiga 4, sun samu miyagun makamai a Katsina. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

"A yayin da dakarun rundunar Operation Hadarin Daji suke kakkabe 'yan bindiga da sauran masu laifi a ranar 4 ga watan Maris 2021, an yi musayar wuta kuma an yi nasarar halaka 'yan bindiga 4, an kwace makamai da babur yayin aukuwar lamarin a lauyen Marina dake karamar hukumar Safana ta jihar Katsina," takardar tace.

“'Yan bindigan da ba a san yawansu ba tare da shanu masu yawa aka hango a kan hanyar Batsari zuwa Runka.

“Amma kuma a yunkurinsu na tserewa dakarun, 'yan bindigan sun dinga harbe-harbe amma zakakuran sojojin sun yi martani cike da kwarewa, hakan yasa 'yan bindigan suka tsere.

“A yayin arangamar, an halaka 'yan bindiga 4 yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika. Sojojin sun samu bindiga Ak-47 2 da babur daya.

“Amma abun takaici shine yadda aka rasa soja daya yayin arangamar. Dakarun sun mamaye yankin kuma suna neman 'yan bindigan da suka tsere."

KU KARANTA: Mutum 101 da ake zargin 'yan Boko Haram ne suna maka FG a kotu, sun bukaci diyyar N303m

A wani labari na daban, nan babu dadewa gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed zai koma jam'iyyar APC, cewar gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum.

Gwamna Zulum ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin bikin saka harsashin sabon gagarumin gidan gwamnatin jihar Bauchi da zai lamushe N6.3 biliyan, Channels TV ta wallafa.

"Bari in sake nuna godiyata ga takwarana gwamnan jihar Bauchi da sauran takwarorina na arewa maso yamma da suke bani goyon baya mai matukar yawa."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel