Mutum 101 da ake zargin 'yan Boko Haram ne suna maka FG a kotu, sun bukaci diyyar N303m
- Mutum 101 da ake zargi da zama 'yan Boko Haram sun maka gwamnatin tarayya a kotu
- Suna zargin gwamnatin da tsaresu a kurkuku tun 2009 ba tare da an mika su gaban kotu ba
- Suna bukatar diyyar N303m, a sakesu kuma kada a sake take musu hakkokinsu na dan Adam
Wasu mutane da aka tsare sakamakon zarginsu da ake yi da zama 'yan Boko Haram sun bukaci wata babbar kotun tarayya da ke zama a Legas da ta kwatar musu hakkinsu na tsaresu tsawon shekaru 12 da aka yi ba tare da an yi musu hukunci ba.
Ta hannun lauyansu Ahmed Adetola-Kazeem na kungiyar kare hakkin 'yan fursuna, suna bukatar kotu ta bada umarnin sakinsu da gaggawa.
Sun kara da mika bukatar a dakatar da wadanda ke zarginsu daga sake take musu hakkinsu na dan Adam a kowacce hanya, The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA: Sojin sama sun sheke gagararren shugaban 'yan bindiga, Rufai Maikaji da mukarrabansa
A karar, akwai antoni janar na tarayya, sifeta janar na 'yan sanda, mai bada shawara kan tsaron kasa da kuma shugaban gidajen gyaran hali na Najeriya.
Masu karar na bukatar a umarci gwamnatin tarayya da ta biya su N303 miliyan na diyyar kama su da tsaresu da tayi ba bisa ka'ida ba.
PRAI ta shigar da karar kare hakkinsu na dan Adam a madadin wadanda ake zargin.
Ta bayyana cewa tsaresu da aka yi a gidajen gyaran hali tun daga watan Yulin 2009 ba bisa ka'ida bane.
An mayar da wadanda ake zargi zuwa jihar Legas a watan Maris na 2011 kuma a halin yanzu suna gidan yarin Kirikiri ba tare da anyi musu shari'a ba.
Sun yi ikirarin cewa an hana su ganin iyalansu da lauyoyinsu.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa FCT, sun bindige mai juna biyu tare da sace mijinta
A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kai wa kauyensu ministan harkokin 'yan sanda, Muhammad Dingyadi, dake karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto farmaki.
A nan suka yi garkuwa da matar babban limamin kauyen. An tattaro bayanai akan yadda 'yan bindiga suka addabi mazabar Dingyadi wacce take da kauyaku a kalla 18 a karkashinta.
An gano cewa 'yan bindigan sun isa kauyen ne a baburansu da daren Laraba ba tare da wasu jami'an tsaro sun dakatar dasu ba.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng