Jami'in soja ne ke samarwa 'yan bindiga alburusai da kakin soja a Zamfara

Jami'in soja ne ke samarwa 'yan bindiga alburusai da kakin soja a Zamfara

- A jihar Zamfara, sojoji sun kame wani soja dake safarar kakin soja da alburusai ga 'yan bindiga

- Rundunar sojan ta kame tare da budurwar sojan a kokarinsu da samarwa 'yan bindiga kayan aiki

- Gwamnatin jihar Zamfara ta nuna kwadayinta ga irin mataki da rundunar ta soja zata dauka akansa

'Yan bindiga da suka addabi jihar Zamfara galibi ana ganinsu cikin kakin sojoji da muggan makamai.

Gwamnatin Zamfara ta ce an kama wani jami’in Sojan Najeriya da ke ba da alburusai da kakin soja ga ‘yan bindiga a jihar, TheCable ta ruwaito.

A wani taron manema labarai a ranar Juma'a, Bashir Maru, mataimakin shugaban ma'aikata na gwamna Bello Matawalle, gwamnan jihar, ya ce sojoji sun kame jami'in tare da budurwar sa, bayan bayanan sirri da aka samu daga al'umma.

KU KARANTA: Buhari ga sabbin Hafsoshin tsaro: Kwanakin kadan gareku ku daidaita kasar nan

Jami'in soja ne ke samarwa 'yan bindiga alburusai da kakin soja a Zamfara
Jami'in soja ne ke samarwa 'yan bindiga alburusai da kakin soja a Zamfara Hoto: KOKO Tv Nigeria
Source: UGC

“Kwanan nan ne sojoji suka damke wani jami’in soja da budurwarsa wadanda ke aikin taimakawa 'yan bindiga da kakin soji da alburusai tare da hadin kan wasu masu yin zagon kasa. Wannan kamun da aka yi ya samu ne ta hanyar samun bayanan sirri daga al'umma," inji shi.

Gwamnatin jihar ta bayyana jiran matakin da rundunar soja zata dauka kan bata-garin da aka kama tare da fidda cikakken bayani a hukumance.

Hakazalika, Bashir Maru yace kamun "ya tabbatar da matsayin Gwamna Bello Mohammed cewa muddin ba a tsarkake yakar 'yan ta'adda daga guragurbi da masu zagon kasa ba, to ba za mu yi samun nasarar da ake so ba a yakin.

“Bari in yi amfani da wannan dama don jinjina wa jajircewa da kishin kasa na mutumin da ya fito da bayanan da suka kai ga kame wadannan mayaudara. Godiyarmu ba ta da iyaka.”

Ba a sami Mohammed Yerima, mai magana da yawun rundunar sojojin ba nan da nan don yin bayani game da kamun.

A watan Fabrairu, 'yan bindiga sun sace daruruwan 'yan mata 'yan makaranta daga makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe a karamar hukumar Talatu-Mafara. An sako ‘yan matan ne kimanin kwanaki 10 bayan sace su.

KU KARANTA: Gobara ta yi kaca-kaca da shahararriyar kasuwar Robobi a garin Onitsha

A wani labarin, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya mayar da martani ga shawarar da Majalisar Tsaro ta Kasa ta yanke na ayyana jihar ta Zamfara a matsayin haramtaccen yanki ga jirage, Daily Trust ta ruwaito.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a karshen taron majalisar tsaron kasa da aka yi ranar Talata.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel