Yanzu Yanzu: Hadimin shugaban kasa ya bayyana lokacin da Buhari zai karbi rigakafin korona
- Za a yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari rigakafin annobar korona
- Kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar, Buhari zai karbi rigakafin ne da karfe 11:30 na safiyar Asabar, 6 ga watan Maris
- Za a yi masa rigafin na AstraZenec a sabon dakin taro na Banquet da ke fadar Villa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi rigakafin annobar korona da na AstraZeneca da karfe 11:30 na safiyar Asabar, 6 ga watan Maris.
Mai taimaka wa shugaban na musamman kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a cikin wani sako da ya wallafa a shafin Twitter.
KU KARANTA KUMA: An cafke wani jami’in rundunar yan sandan Nigeria bisa laifin satar bindigogi 5 AK-47
A kokarin samar da karin bayani kan ci gaban, Ahmad ya wallafa zane mai zane wanda ke nuna cewa za a yi wa shugaban rigakafin ne a sabon dakin taro na Banquet na fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.
KU KARANTA KUMA: Ina da tabbacin Buhari ba bacci yake ba, Jonathan a kan rashin tsaron Najeriya
A gefe guda, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Juma’a ya bayyana cewa ya yi gwajin kwayar cutar Coronavirus, Daily Trust ta ruwaito.
Ya sanar da labarin ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake magana a wani taron tattaunawa da aka shirya don bikin cikawarsa shekaru 84 da haihuwa.
Shirin an gudanar dashi ne a cikin dakin karatun shugaban kasa na Olusegun Obasanjo (OOPL), Abeokuta.
A wani labarin, Shugaban jami’ar Adeleke, Farfesa Solomon Adebiola, ya bayyana cewa riga-kafin kwayar cutar COVID-19 da masana kimiyya na Najeriya suka kirkiro a halin yanzu tana matakin gwaji na asibiti, Vanguard News ta ruwaito.
Ya kara da cewa allurar, wacce Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da ita kuma ta sami goyon bayan Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta samu ne daga wani masanin kimiyya daga Jami’ar Adeleke, Dokta Oladipo Kolawole, tare da hadin gwiwar wasu daga wasu jami’o’i biyar na kasar.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng