An cafke wani jami’in rundunar yan sandan Nigeria bisa laifin satar bindigogi 5 AK-47

An cafke wani jami’in rundunar yan sandan Nigeria bisa laifin satar bindigogi 5 AK-47

- An cafke wani dan sanda mai suna Shedrack Igwe da laifin satar bindigogi

- An kama Jami’in Igwe wanda ke aiki tare da rundunar ‘yan sanda na Abia a Ebonyi inda ya gudu bayan ya saci bindigogin

- Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ebonyi ya tabbatar da faruwar wannan al'amari

An damke Shedrack Igwe, wani jami’in dan sanda a jihar Abia da ake zargi da satar akalla bindigogi AK-47 daga sashin rundunonin ajiye makamai na MOPOL Base 28, Umuahia, inda yake aiki.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Igwe wanda dan sanda ne ya saci bindigogin tare da taimakon wasu wadanda har yanzu ba'a bayyana sunayensu ba.

Legit.ng ta tattaro cewa ya saci bindigogin ne a ranar Talata, 2 ga watan Maris, sannan ya tsere zuwa jihar Ebonyi, mahaifar sa, inda daga baya hadaddiyar tawagar ‘yan sanda daga jihohin Abia da Ebonyi suka kama shi.

An cafke wani jami’in rundunar yan sandan Nigeria da laifin satar bindigogi 5 AK-47
An cafke wani jami’in rundunar yan sandan Nigeria da laifin satar bindigogi 5 AK-47 Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Zamfara na jiran ganin matakin da rundunar soji za ta dauka kan sojan da ke kai wa yan bindiga kayayyaki

An kwato bindigogin AK-47 guda biyar daga garinsa yayin da aka mayar da shi zuwa ga rundunar 'yan sanda ta jihar Abia don gudanar da bincike.

An ce jami'in ya yi amfani da kudin da ya samu daga siyar da bindigogin da ya sata ya sayi sabbin babura uku don yi achaba.

Duk da cewa kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Abia ya ki cewa uffan kan lamarin, an ce kwamishinan' yan sandan jihar Ebonyi ya tabbatar da faruwar al'amarin.

Kwamishinan ‘yan sanda na Ebonyi, Aliyu Garba, ya ce rundunarsa ta taimaka wa rundunar ta Abia wajen kamewa da kwato bindigogin, ya kara da cewa, rundunar ta Abia ce za ta iya bayar da cikakken bayani game da lamarin.

KU KARANTA KUMA: Mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano: Babu hannunmu a hana zaman, gwamnatin Kano

A wani labarin, mun ji cewa 'Yan bindiga da suka addabi jihar Zamfara galibi ana ganinsu cikin kakin sojoji da muggan makamai.

Gwamnatin Zamfara ta ce an kama wani jami’in Sojan Najeriya da ke ba da alburusai da kakin soja ga ‘yan bindiga a jihar, TheCable ta ruwaito.

A wani taron manema labarai a ranar Juma'a, Bashir Maru, mataimakin shugaban ma'aikata na gwamna Bello Matawalle, gwamnan jihar, ya ce sojoji sun kame jami'in tare da budurwar sa, bayan bayanan sirri da aka samu daga al'umma.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng