Ina da tabbacin Buhari ba bacci yake ba, Jonathan a kan rashin tsaron Najeriya

Ina da tabbacin Buhari ba bacci yake ba, Jonathan a kan rashin tsaron Najeriya

- Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasan Najeriya ya bukaci hadin guiwar Buhari, gwamnoni da masu ruwa da tsaki wurin yakar rashin tsaro

- Tsohon shugaban kasar yace yana da tabbacin Buhari da gwamnonin kasar nan basu bacci a kan matsalar tsaron da ta addabi kasar nan

- Jonathan ya sanar da hakan ne yayin da suka kai ziyarar ta'aziyyar mutuwar mahaifin gwamnan jihar Delta

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya hada kai da gwamnoni, shugabanni tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wurin shawo kan matsalar tsaron kasar nan.

Jonathan yayi wannan kiran ne yayin da ya jagoranci wasu wakilan siyasa daga Bayelsa zuwa ta'aziyya ga Gwamna Ifeanyi Okowa a gidan gwamnatin Asaba na jihar Delta a kan rasuwar mahaifin gwamnan.

Ya ce abun takaici ne yadda ake sace yaran makarantu da sauran 'yan Najeriya, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Yadda jiragen sama ke wurgawa 'yan bindiga makamai da abinci a Zamfara

Ina da tabbacin Buhari ba bacci yake ba, Jonathan a kan rashin tsaron Najeriya
Ina da tabbacin Buhari ba bacci yake ba, Jonathan a kan rashin tsaron Najeriya. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Ina da tabbacin idan gwamnoni da gwamnatin tarayya suka mayar da hankali, zamu iya shawo kan matsalar rashin tsaro a kasar nan.

"Ina da tabbacin shugaban kasa baya bacci kuma gwamnonin kasar nan basu bacci a kan kalubalen tsaron kasar nan.

“Matukar gwamnoni, shugaban kasa da dukkan hukumomin tsaro za su yi aiki tare, Najeriya za ta iya tsallake wannan mummunan kalubalen da take fuskanta," yace.

A yayin jinjinawa shugaban kasa a kan kokarinsa na shawo kan matsalar tsaro, Jonathan ya bukaci 'yan Najeriya da su hada karfi da karfe wurin fatattakar rashin tsaro.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kutsa garinsu ministan 'yan sanda, sun sheke 1 tare da sace matar babban limami

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kisan da aka yi wa daya daga cikin shugabannin kuma gagararren dan bindiga mai suna Rufai Maikaji tare da sama da 'yan bindiga dari dake karkashinsa.

Labarin mutuwar Maikaji ta fasu ne bayan kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar da ita a wata takarda.

Kamar yadda takardar ta sanar, Maikaji tare da daruruwan 'yan bindiga sun sheka lahira bayan samamen da sojin sama suka kai a dajin Malul da ke karamar hukumar Igabi ta jihar.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng