Wata uwa mai yara biyu ta mutu yayinda take tsaka da holewa da saurayinta a Yola

Wata uwa mai yara biyu ta mutu yayinda take tsaka da holewa da saurayinta a Yola

- Yan sanda sun damke wani magidanci bayan mutuwar budurwarsa wacce ta kai masa ziyara

- Masoyiyar tasa wacce ke da 'ya'ya biyu ta mutu a yayinda suke tsaka da holewa

- Ana kan bincike domin gano ainahin abunda ya kashe matar

Wata mata mai shekaru 37 wacce ked a haihuwar ‘ya’ya biyu ta mutu yayin holewa da masoyinta a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Yan sanda sun kama masoyin nata mai suna Lekan Agboola, wanda ya kasance injiniya a kamfanin sadarwa.

DSP Suleiman Nguroje, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Adamawa, ya ce Agboola, wanda a yanzu haka yake tsare a sashin binciken manyan laifuka na rundunar, yana da mata da yara biyu, suna zaune a Legas.

Wata uwa mai yara biyu ta mutu yayinda take tsaka da holewa da saurayinta a Yola
Wata uwa mai yara biyu ta mutu yayinda take tsaka da holewa da saurayinta a Yola Hoto: @PremiumTimesng
Source: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Agboola ya furta cewa marigayiyar ya kasance budurwarsa fiye da shekaru uku.

KU KARANTA KUMA: An cafke wani jami’in rundunar yan sandan Nigeria bisa laifin satar bindigogi 5 AK-47

Da yake bayanin abin da ya faru a ranar da ta mutu, Agboola ya ce, “A ranar 24 ga Fabrairu, 2021, da misalin karfe 9 na safe, na kira ta a waya na ce ta zo ta gan ni saboda ba mu ga juna ba na wani lokaci. Lokacin da ta iso, mun fara holewa sai kwatsam ta faɗi.

“Lokacin da na fahimci ba ta numfashi, sai na kira daya daga cikin abokaina mata na fada mata abin da ya faru. Ta shawarce ni da in kai ta asibiti inda aka tabbatar da cewa ta mutu.”

Nguroje ya ce ‘yan sanda na kokarin binciken ainihin abin da ya sa matar ta mutu.

KU KARANTA KUMA: Mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano: Babu hannunmu a hana zaman, gwamnatin Kano

A wani labarin, tsohuwar matar tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigon jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode, Precious Chikwendu ta maka tsohon mijinta a gaban kotu da bukatar karbar 'ya'yan da suka haifa.

Precious ta maka Fani-Kayode a gaban wata babban kotun tarayya dake Abuja inda take bukatar karbar 'ya'yanta hudu da suka haifa yayin da suke tare, amma a bar mahaifinsu ya dinga zuwa ganinsu, The Nation ta wallafa.

Matar mai son Fani-Kayode da duk wasu mukarrabansa su kiyayi kwace mata 'ya'yanta ta karfi da yaji, ta bukaci kotun da ta sa tsohon ministan ya dinga biyanta N3.438 miliyan duk wata domin kula da yaran tare da wasu kudi na daban domin karatunsu da sauran bukatunsu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel