Ana tattaunawa da shugabannin 'yan bindiga don kawo zaman lafiya a Niger

Ana tattaunawa da shugabannin 'yan bindiga don kawo zaman lafiya a Niger

- Gwamnatin jihar Niger na son tattaunawa da yan fashin jihar don kawo zaman lafiya mai dorewa a jihar

- Kwamandojin 'yan fashin sun fara tattaunawa da 'yan uwansu kan lamarin a yau juma'a

- Gwamnatin jihar tace a shirye take ta fara tattaunawa da su da zarar sun gama nasu taron

Kwamandojin 'yan fashi daban-daban dake ta'addanci a jihar Niger sun yi taro akan yadda za'a samu maslaha da gwamnatin jihar.

Jaridar The Nation ta gano cewa anyi taron yau juma'a a karamar hukumar Shuroro, jihar Niger.

Taron wanda masu shiga tsakanin ɓangarorrin biyo suka kira ya samu halartar da yawa daga cikin shugabannin 'yan bindigan jihar.

Saidai bangaren gwamnati basu samu halartar taron ba.

KARANTA ANAN: Jami'in soja ne ke samarwa 'yan bindiga alburusai da kakin soja a Zamfara

A kwanan baya gwamnatin jihar ta bayyana aniyarta na tattaunawa da fulani makiyaya da 'yan fashi don kawo dawwamammen zaman lafiya.

Ana tattaunawa da shugabannin 'yan fashi don kawo zaman lafiya a Niger
Ana tattaunawa da shugabannin 'yan fashi don kawo zaman lafiya a Niger Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Buhari ga sabbin Hafsoshin tsaro: Kwanakin kadan gareku ku daidaita kasar nan

Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matene ya tabbatar da anyi taron amma babu wakilan gwamnati a wajen.

"Ɗaya daga cikin shugabannin masu shiga tsakani ya kira taron don tattaunawa yadda za'a kawo zaman lafiya a jihar," a cewar sakataren.

"Amma taron nasu ne su kadai kuma sun tattauna yadda za'a kawo zaman lafiya a jihar," inji sakataren

Ya kuma ƙara da cewa da zaran sun gama zamu shiga tattaunawa dasu don musan yadda za'a ɓullo ma lamarin.

A wani labarin kuma Kotu ta dakatar da muƙabalar da aka shirya yi da Sheikh Abdul-Jabbar a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da mukabalar da ta yi shirin yi tsakanin Sheikh Abdul-Jabbar Nasir Kabara da malaman jihar Kano a ranar Lahadi

Hakan ya biyo bayan umurnin da wata kotun Majistare da bada ne na dakatar da mukabalar bisa bukatar da wani lauya mai zaman kansa ya shigar a kotun.

Ahmad Yusuf dan mtan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Online view pixel