Buhari ga sabbin Hafsoshin tsaro: Kwanakin kadan gareku ku daidaita kasar nan
- Shugaban kasar Najeriya ya kalubanci shugabannin hafsoshin soja da su kubutar da Najeriya
- Shugaban ya bayyana basu kankanin lokaci don tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar baki daya
- Hakazalika ya umarce su da su gudanar da aikinsu a madadinsa tunda shine babban kwamanda
Yayin da kasar ke fama da manyan matsalolin tsaro da ke fuskantar tattalin arzikinta, Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a ya bukaci sabbin shugabannin hafsoshin kasar da su yi duk abin da za su iya wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.
Da yake jawabi yayin kawata su, Buhari ya bukace su da su isar da kasar ga tudun na tsira, lura da cewa suna da kankanin lokacin yin hakan, Vanguard News ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Buhari ya ce:
“A lokacin tattaunawarmu ta tsaro ta tsawon awanni hudu, ranar Talata, na dauki nauyi a matsayin babban kwamanda domin ku fita filin daga da kuma tabbatar da kasar ta kubuta.
“Kuna da 'yan makwanni kadan domin yin hakan saboda lokacin damina, muna sa ran mutane su bunkasa karfin gwiwa su koma gona, don kar mu fada cikin matsala ta hanyar nisanta daga filin gona ta yadda ba za mu iya samar da wadataccen abinci ba ga al'umma."
KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar Sabo a jihar Oyo
Ya gaya wa shugabannin hafsoshin da su ga nadin nasu, tabbatar da su da kuma kawata su a matsayin kuri'ar amincewa a kansu.
"Ga wadanda (daga cikin ku) da aka tabbatar a wannan bikin kawatawar, a gaban matan ku, wani karin kwarin gwiwa ne da aka bayyana akan ku a madadin kasar don magance matsalar rashin tsaro da kasar ke ciki, kuma al'umma na neman taimakonku cikin gaggawa."
Ya kuma ba su tabbacin goyon bayansa sosai yayin da suke sauke nauyin da aka dora musu.
“Na yarda da alhakin abubuwan da zaku aikata a fagen daga; ya rage naku ne ku zakulo kwararrun jami'anku ba tare da la'akari da manya ko cancantar takardu ba ku tura su don tabbatar da cewa mun amintar da kasar nan.
"Dukanmu muna fatan ku yi rawar gani kuma ni a matsayin Babban Kwamanda, ina mara muku baya dari bisa dari, kuma ina tsammanin za ku yi amfani da jami'ai da mazajen ku yadda ya kamata don tabbatar da kasar ta tsira," in ji Shugaban.
Da yake amsawa a madadin sauran shugabannin hafsoshin, Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor ya bai wa Shugaban kasa tabbacin cewa ba za su gaza a kan aikinsu ba kamar yadda doka ta ba su a sarari.
“Najeriya za ta sake samun zaman lafiya. Dangane da umarni, za mu magance dukkan matsaloli, tare da aiki da duk sauran kungiyoyin tsaro,” inji shi.
Sauran wadanda aka kawatan sun hada da Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a matsayin shugaban hafsan sojan kasa, da mataimakin Admiral Awwal Gambo a matsayin shugaban hafsan sojin ruwa da Air Marshal Isiaka Amao a matsayin shugaban hafsan sojin sama.
KU KARANTA: Gobara ta yi kaca-kaca da shahararriyar kasuwar Robobi a garin Onitsha
A wani labarin, Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin sabbin shugabannin rundunonin soja bayan bin diddigin rahoton Kwamitin Tsaro wanda ya bayar da shawarar tabbatar da su, The Nation ta ruwaito.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Laraba da ta gabata ya mika bukatar Shugaba Muhammadu Buhari na tabbatar da sabbin hafsoshin tsaron, ga kwamitin tsaro.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng