Gobara ta yi kaca-kaca da shahararriyar kasuwar Robobi a garin Onitsha

Gobara ta yi kaca-kaca da shahararriyar kasuwar Robobi a garin Onitsha

- Wata gobara ta lakume wani sashi na kasuwar robobi a garin Onitsha da safiyar Juma'a

- Rahotanni sun bayyana cewa, ba a samu asarar rai ko rauni kasancewar babu kowa yayin gobarar

- Hakazalika, an ruwaito gaggauta kashe gobarar tare da girke 'yan sanda don hana sace-sace

Gobara ta lakume shahararriyar Kasuwar robobi da ke Onitsha a jihar Anambra a safiyar ranar Juma’a.

Daily Trust ta tattaro cewa ba a samu asarar rai ba, domin a lokacin da lamarin ya faru babu wanda ke cikin kasuwar.

An kuma tattaro cewa gobarar ta fara ne a ranar Juma’a da misalin 1:50 na safe.

Lamarin gobarar ya faru ne a wani gini da ke Kasuwar Robobi.

KU KARANTA: Makiyaya 2 da suka bata sun gamu da ajalinsu a Zangon Kataf

Gobara ta yi kaca-kaca da shahararriyar kasuwar Robobi a garin Onitsha
Gobara ta yi kaca-kaca da shahararriyar kasuwar Robobi a garin Onitsha Hoto: Vanguard News
Source: UGC

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda ta jihar Anambara, CSP Haruna Mohammed ya ce jami'an 'yan sanda karkashin jagorancin DPO na ofishin 'yan sandan Onitsha, SP Ifeanyi Iburu sun hanzarta zuwa wurin da lamarin ya faru.

Hakazalika ya kuma bayyana cewa sun kewaye yankin kasuwar don hana sace-sace da kuma haifar da wata masifa.

A cewarsa, an kuma tuntubi hukumar kashe gobara kuma sun yi gaggawar zuwa wurin da abin ya faru.

”An kashe wutar tare da taimakon jami’an kashe gobara da sauran jama;ar yankin. Ba a samu asarar rai ko rauni ba. Ana ci gaba da bincike don tabbatar da irin barnar da yanayin da gobarar ta haifar,” inji shi.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Gombe ya nada sabon Mai Tangale

A wani labarin, Wuta a tsakar dare ta yi kaca-kaca da kasuwar Sabo da ke garin Oyo, Jihar Oyo. Wadanda abin ya faru a kan idanunsu sun shaida wa Premium Times cewa kayayyaki da dukiyoyi na biliyoyin nairori sun lalace yayin gobarar.

Gobarar, wacce aka ruwaito ta fara ne da misalin karfe 10:00 na dare, ta yadu zuwa mafi yawan sassan kasuwar ta Sabo. Wasu 'yan kasuwa, wadanda shagunansu da kayayyakinsu masu dunbun daraja suka kone, an ce suna kukawa kan lissafa asarar da suka yi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel