Tsohuwar ƴar majisa Daga jihar Gombe ta ɗauki nauyin karatun ɗalibai 540

Tsohuwar ƴar majisa Daga jihar Gombe ta ɗauki nauyin karatun ɗalibai 540

- Tsohuwar 'yar majlisar wakilai ta kasa, Hon. Fatima Bello, dake wakiltar mazaɓun Kaltungo/Shongom a jihar Gombe ta ƙaddamar da wani shiri da zai dauki nauyin karatun ɗalibai 540.

-Ana sa ran shirin zai laƙume kudi 10.8 miliyan wajen tallafawa ɗalibai masu karatu a makarantun gaba da sakandire

-Ta ɗauki nauyin ɗaliɓai ƴan asalin kudancin jihar ta Gombe

Wata tsohuwar ƴar majalisa daga mazabar Kaltungo/Shongom, a jihar Gombe, Fatima Binta Bello ta bada tallafin karatu na 10.8 miliyan a mazaɓarta.

Tallafin zai ɗauƙi nauyin karatun ɗalibai yan asalin mazaɓar kimanin mutum 540 kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: NAFDAC ta amince ayi amfani da rigakafin Astrazeneca a Najeriya

A jawabin da tayi lokacin da ta ƙaddamar da shirin Hon. Binta tace, ta dauki wannan matakine don ƙarfafa neman ilimi tsakanin matasan yankin maza da mata.

Ta ƙara da cewa: "Da yawan talakawa basa iya biyan kuɗin karatun 'yayansu, ga kuma sauran abubuwa na yau da kullum."

Tsohuwar ƴar majisa Daga jihar Gombe ta ɗauki nauyin karatun ɗalibai 540
Tsohuwar ƴar majisa Daga jihar Gombe ta ɗauki nauyin karatun ɗalibai 540 Hoto: @Bua_education
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Gobara ta yi kaca-kaca da shahararriyar kasuwar Robobi a garin Onitsha

"Ina fatan wannan tallafin zai rage raɗaɗin da iyaye ke shiga musamman waɗan da 'ya'yansu ke karatu a makarantun gaba da sakandire," a cewarta.

Hon. Binta ta ƙara jaddada ƙudirinta wajen ƙoƙarin tallafa ma marasa ƙarfi musamman matasa wajen samar musu da ayyuka, tallafin ilmi, da sauran mu'amalolin rayuwa.

Ɗaya daga cikin ɗaliban da suka ci muriyar shirin, Dauda Awak, ya yabama Hon. Binta a kan goyon bayan da take basu.

Kuma yace wannan tallafin zai matuƙar taimaka musu wajen fuskantar ƙalubalen da suke fusakanta a makaranta.

A wani labarin kuma Jam’iyyar APC ta yi babban kamu na jigon PDP a jihar Yobe

Babban jigon jam’iyyar PDP a jihar Yobe, Baba Abba-Aji ya sauya sheka zuwa APC

Tsohon dan takarar na mataimakin Gwamnan PDP a zaben 2019 ya ce ci gaban da aka samu a karkashin Buni ne ya ja hankalinsa

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Online view pixel