Da Ɗumi-Ɗumi: NAFDAC ta amince ayi amfani da rigakafin Astrazeneca a Najeriya
- Bayan shigowar rigakafin corona ta Astrazeneca an ba NAFDAC wasu domin yin aikinta
- Hukumar ta tabbatar da ingancin allurar yau, kuma ta bada damar ayi ma yan ƙasa
- Hukumar lafiya ce ta bayyana haka da safiyar yau a shafinta na twitter
Hukumar kula da abinci da kwayoyi ta ƙasa (NAFDAC) ta amice ayi ma yan Najeriya rigakafin Astrazeneca wanda aka tabbatar da isowar ta Najeriya tun a ranar talata data wuce.
A rahoton da jaridar Punch ta wallafa tace, hukumar lafiya ta ƙasa ce ta bayyana haka a shafinta na Twitter.
KARANTA ANAN: Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Qur'ani
Sakon data wallafa yace: "Bayan kammala dukkan gwaje-gwaje, hukumar (NAFDAC) ta amice ayi allurar kuma ta tabbatar mana da cews gwajin da tayi ya bada sakamako mai kyau."
KARANTA ANAN: Gwamnonin Arewa maso gabas sun soki aikin Mambilla, sun ce a takarda ake kwangilar
"Yanzun Najeriya nada damar yin amfani da allurar rigakafin 3.9 miliyan da take dashi. Anyi ma shirin take da #YesToCOVID19Vaccine"
Tun ranar Talata da rigakafin ta iso, an bama NAFDAC wasu don tayi gwaje-gwajen ta don tabbatar da ingancin allurar.
Da wannan sakamakon gwajin ne, hukumar lafiya ke da damar fara yi ma ƴan Najeriya allurar rigakafin wanda aka tsara za'a fara yima ma'aikatan lafiya a sashen duba mara lafiya dake asibitin ƙasa a Abuja.
A wani labarin kuma NGF ta bayyana ranar da za'a yi ma gwamnoni allurar rigakafin corona
Bayan faɗin ranar da za'ayi ma shugaban ƙasa da mataimaƙinsa, suma gwamnoni sunce ashirye suke ayi musu
Mai magana da yawun ƙungiyar ya ɓayyana haka jim kadan bayan taron da gwamnoni suka yi
Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.
Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd
Asali: Legit.ng