NGF ta bayyana ranar da za'a yi ma gwamnoni allurar rigakafin corona
- An tabbatar da isowar allurar rigakfin Astrazeneca kimanin 3.9 miliyan cikin ƙasa kamar yadda shugaban hukumar lafiya ya bayyana
- Bayan faɗin ranar da za'ayi ma shugaban ƙasa da mataimaƙinsa, suma gwamnoni sunce ashirye suke ayi musu
- Mai magana da yawun ƙungiyar ya ɓayyana haka jim kadan bayan taron da gwamnoni suka yi
Ƙungiyar gwamnonin ƙasar nan ta bayyana ranar da za'a yi ma mambobinta allurar rigakafin cutar corona.
Ƙungiyar ta ayyana ranar 10 ga watan maris, a matsayin ran da za'a yi musu allurar tare da mataimakansu.
A taronsu na yau, dukkansu sun yarda zasu bi duk wasu ƙa'idoji da masana kiwon lafiya suka gindaya. Daga cikin dokokin akwai fara yiwa jami'an lafiya allurar rigakafin.
KARANTA ANAN: Shugaban Majalisa ya ce manyan dillalan miyagun ƙwayoyi ke ɗaukan nauyin ƴan bindiga
Kamar yadda jaridar Punch ta wallafa a shafinta, wannan na daga cikin abubuwan da suka tattauna a loƙacin taron ƙungiyar yau.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ne ya jagoranci taron wanda ya gudana ta hanyar amfani da fasahar zamani.
KARANTA ANAN: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a Katsina sun halaka da dama
Shugaban yaɗa labaran ƙungiyar, Abdulrazaque Bello- Barkindo, ya tabbatar da haka a Abuja.
Bello- Barkindo ya kara da cewa, an amince shuwagabanni da kuma ma'aikatan lafiya, su za'a fara yi ma rigakafin.
A cewarsa: "Gwamnonin sun amince suyi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da gwamnatin tarayya don horas da wanda za suyi aikin, da kuma bama allurar rigakafin ingataccen tsaro."
An yi kira ga ƴan najeriya da su yi amfani da kafar da aka buɗe dan yin registar amsar rigakafin cutar.
A wani labarin kuma Nan babu dadewa zaka dawo jam'iyyar APC, Zulum ga Gwamnan Bauchi
Zulum ya sanar da hakan ne yayin da yaje gagarumin bikin saka harsashin ginin sabon gidan gwamnatin Bauchi
Gwamnan Bornon ya bayyana irin cigaban da ake samu a yankin a karkashin kungiyar gwamnonin arewa maso gabas
Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.
Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd
Asali: Legit.ng