'Yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a Katsina sun halaka da dama

'Yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a Katsina sun halaka da dama

- Sojoji da dama sun rasa rayukansu bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai musu a sansaninsu a Katsina

- Al'amarin ya faru ne da misalin 1pm na ranar Alhamis a karamar hukumar Safana da ke jihar Katsina

- 'Yan ta'addan sun ragargaji sojojin ne yayin da suka koma sansaninsu bayan sun kammala wani aikinsu a wani daji

Sojoji da dama sun rasa rayukansu bayan wasu 'yan bindiga sun kai wa sansaninsu da ke Marina hari a karamar hukumar Safana da ke jihar Katsina, rahoton Daily Trust.

Lamarin ya faru da misalin karfe 1 na rana, ranar Alhamis kamar yadda ganau suka tabbatar.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da AK-47

'Yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a Katsina sun halaka da dama
'Yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a Katsina sun halaka da dama. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Duk da dai ba a tabbatar da yawan sojojin da suka rasa rayukansu sakamakon harin ba, amma ana zargin suna da yawa.

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

Sojojin suna hanyarsu ta dawowa daga aikinsu da sukayi a wani daji kawai suka ji saukar makamai ta ko ina.

Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce: "Sojojin basu san cewa 'yan bindigan sun boye a sansaninsu ba. Suna isa suka hau ragargazarsu.

"Abin takaicin shine yadda sojojin suka dawo daga wani aiki da suka yi wanda suka samu nasara mai yawa, sunyi kaca-kaca da wasu 'yan bindiga ashe zasu riski ajalinsu a sansaninsu," kamar yadda yace.

Wani mazaunin yankin ya kara da bayyana yadda sojojin suka kashe 'yan bindiga biyu lokacin da suke musayar wuta.

Anyi kokarin ji daga bakin hukumar 'yan sanda ko soji amma hakan bai yiwu ba.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel