Yadda jiragen sama ke wurgawa 'yan bindiga makamai da abinci a Zamfara
- Bincike ya nuna cewa jiragen sama ke jefawa 'yan bindiga makamai da abinci a jihar Zamfara
- Ana amfani da jiragen saman wurin safarar zinaren da aka haka ba bisa ka'ida ba a jihar Zamfara
- A ranar Talata ne Buhari ya yanke hukuncin hana jiragen sama wucewa ta jhar Zamfara
Jiragen sama da ke samar da makamai tare da abinci ga 'yan bindiga shine babban dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta hana jiragen sama bi ta jihar Zamfara, an gano hakan a ranar Laraba.
Baya ga haka, ana amfani da jiragen saman wurin safarar zinarin da aka haka ba bisa ka'ida ba a jihar.
Gwamnatiin tarayya ta haramtawa jiragen sama bi ta jihar Zamfara a ranar Talata bayan taron da aka yi na tsaron kasa.
Ta kara da haramta dukkan hakar ma'adanai na jihar har sai baba ta gani, The Nation ta wallafa.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa FCT, sun bindige mai juna biyu tare da sace mijinta
Majiyoyin tsaro masu yawa a jiya sun bayyana cewa: "Akwai bayanan sirri masu tarin yawa da suke sanar da cewa 'yan bindiga na samun makamai daga jiragen sama.
"Ganin cewa dukkan jihar Zamfara a rufe take yasa wannan bayanin sirrin ya tabbata. Hana wucewar jiragen sama ta jihar ne zai dakile 'yan bindigan sannan dakarun soji su shiga su fitar dasu."
Wannan hukuncin saboda tsaro ne kadai ba siyasa tasa aka yanke shi. An yanke shi ne domin inganta tsaron jihar da yankin baki daya.
KU KARANTA: Daliban Jangebe sun ce da maigadin makarantarsu aka hada kai wurin sacesu, Matawalle
A wani labari na daban, jam'iyyar PDP ta zargi APC da kulle-kullen kwace jihar Zamfara sakamakon rashin tsaron da yake addabar jihar a cikin kwanakin nan.
Kakakin jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya gabatar da korafin a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.
Dama gwamna Bello Matawalle na jam'iyyar PDP ne yake shugabantar jihar dake arewa maso yamma, Premium Times ta wallafa.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng