Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa FCT, sun bindige mai juna biyu tare da sace mijinta

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa FCT, sun bindige mai juna biyu tare da sace mijinta

- Masu garkuwa da mutane sun kutsa Kwaita da ke Kwali inda suka bindige mai juna biyu tare da kwashe mutane 2 da mijinta

- An gano cewa miyagun sun isa yankin wurin karfe 11 na daren Laraba inda suka dinga ruwan wuta

- Kakakin rundunar 'yan sandan FCT, ASP Maryam Yusuf tace 'yan sanda sun ceto mutum 1 kuma wani jami'insu ya samu rauni

Wasu 'yan bindiga sun kai samame a yankin Kwaita da ke Kwali a babban birnin tarayya a Abuja inda suka harbe mace mai juna biyu kuma suka tisa keyar mutum 3 da suka hada da mijinta.

Wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a boye sunansa, ya sanar da Daily Trust cewa lamarin ya faru ne wurin karfe 11 na daren Laraba.

Ya ce masu garkuwa da mutanen sun kutsa gidajen inda suka kwashesu yayin da suka dinga harbe-harbe.

Ya ce harsashin da aka harba ne ya samu matar mai juna biyu. "Dukkan mazauna yankin sun fada dimuwa da fargaba saboda harbe-harben.

KU KARANTA: Daliban Jangebe sun ce da maigadin makarantarsu aka hada kai wurin sacesu, Matawalle

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa FCT, sun bindige mai juna biyu tare da sace mijinta
Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa FCT, sun bindige mai juna biyu tare da sace mijinta
Asali: Original

"Sun so tafiya da matar amma sai suka gane cewa sun sameta da harsashi sannan tana da juna biyu, hakan yasa suka kyaleta," a cewarsa.

Ya ce an kai matar mai juna biyu wani asibiti da ke Gwagwalada domin samun tallafin likitoci.

A yayin amsa tambayoyi, ASP Maryam Yusuf, kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayyar, ta ce 'yan sandan sun yi nasarar ceto mutum daya bayan musayar wuta da 'yan bindigan.

Ta ce a yayin fatattakar 'yan bindigan ne wani dan sanda ya samu rauni.

Yusuf ta kara da cewa, a halin yanzu ana ta kokarin ganin an damko masu garkuwa da mutanen kuma an ceto wadanda suka sace.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram da 'yan bindiga masu gwagwarmayar nemawa arewa 'yanci ne, Adamu Garba

A wani labari na daban, Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya bayyana cewa sun yanke hukuncin yin sasanci shi da takwaransa na jihar Bauchi domin samun hanyar shawo kan lamurran da ke ci wa mutane kwarya a kasar nan.

Kafin nan, dukkan gwamnonin sun dinga tada kayar baya inda suke caccakar junansu a kan rikicin makiyaya da manoma, Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Ortom ya zargi Mohammed da bayyana goyon bayansa ga Fulani da ke yawo da makamai yayin da ya zargesa da zama cikin kungiyar 'yan ta'addan da ke addabar kasar nan.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel