Daliban Jangebe sun ce da maigadin makarantarsu aka hada kai wurin sacesu, Matawalle
- Gwamnan Zamfara ya sanar da cewa maigadin makarantar Jangebe yana daya daga cikin wadanda aka hada kai dasu wurin sace yaran
- Gwamnan ya bayyana cewa 'yammatan sun sanar da hakan a gaban kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara
- Ya tabbatar da cewa za a bincika a gane sahihancin zancen kafin a dauka mataki a kansa tare da sauran wadanda aka hada kai dasu
Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara ya ce 'yammatan Jangebe sun bayyana cewa maigadinsu na makaranta yana daga cikin wadanda aka hada kai dasu aka sacesu.
A ranar Laraba da ta gabata ne Matawalle ya bayyana a shirin siyasarmu a yau na gidan Talabijin na Channels.
Sama da dalibai 270 ne aka sace a makarantar gwamnati da ke garin jangebe na karamar hukumar Talata-Mafara da ke Zamfara a watan Fabrairu. An sako su a ranar Talata.
KU KARANTA: 'Yan Boko Haram da 'yan bindiga masu gwagwarmayar nemawa arewa 'yanci ne, Adamu Garba
A yayin da aka bukaci ya bayyana wadanda suka sace yaran, gwamnan yace 'yan bindigan sun sanar da cewa har da maigadin suka hada baki.
Matawalle yace ana bincike a kan haka amma bai sanar da sauran wadanda aka hada kai dasu ba.
"Har da maigadin makarantar. Yaran sun sanar da hakan kuma sun ce bayan an sakesu, 'yan bindigan sun ce su gaishe musu da maigadin makarantarsu," yace.
"Sun kara da bayyana sunansa a matsayin wanda ya ce su zo a lokacin su kwashe yaran, don haka da hannunsa a ciki.
"Sun sanar da hakan a gaban kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara, za a yi bincike a kan hakan sannan a gano dukkan wadanda ke da hannu a ciki."
KU KARANTA: Gara mu yi asarar kayan, 'Yan kasuwan arewa sun yi martani kan hana kudu kayan abinci
A wani labari na daban, gidauniyar cigaba ta Kwankwasiyya (KDF) ta yi bayanin cewa ta tura a mutum 370 karatun digiri na biyu da na uku a jami'o'in kasashen ketare don ta basu damar samun gogayya a duniya.
Shugaban gidauniyar kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana hakan a cikin ranakun karshen mako a wani taro da yayi da sabbin dawowa daga karatu a kasashen ketare.
Ya ce abinda yasa suke zabar jami'o'in ketare shine bai wa daliban damar gogewa ta yadda za su iya fito na fito da sa'o'insu a duniya, Daily Trust ta wallafa.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng