Zan yi murabus matukar hakan zai kawo karshen satar mutane, Matawalle

Zan yi murabus matukar hakan zai kawo karshen satar mutane, Matawalle

- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle yace in har yin murabus dinsa zai samar da tsaro toh a shirye yake don yin hakan

- Gwamnan ya sanar da hakan ne a wani shirin siyasarmu a yau da aka tattauna da shi kan sace mutane da ake yi a jiharsa

- Matawalle yace baya iya bacci saboda jama'ar jiharsa kuma shi ba ido rufe yake kaunar mulki ba

Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya ce ya shirya tsaf domin yin murabus idan hakan zai kawo karshen rashin tsaro a jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a wani shirin siyasarmu a yau wanda gidan talabijin na Channels TV ya shirya a ranar Laraba.

Ya ce: "Ban damu ba. Idan na san murabus dina a matsayin gwamna zai sa jama'a su kwanta bacci idanunsu biyu rufe, zan sauka daga mulkin.

"A shirye nake in yi abinda zai kawo tsaro. Bana yunwar mulki. Bana iya bacci saboda son baiwa jama'ar Zamfara kariya."

KU KARANTA: Abinda yasa muke kai yara karatu kasashen ketare, Kwankwasiyya

Zan yi murabus matukar hakan zai kawo karshen satar mutane, Matawalle
Zan yi murabus matukar hakan zai kawo karshen satar mutane, Matawalle. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Wannan tsokacin na gwamnan na zuwa ne kwana daya bayan 'yan bindiga sun sako 'yammata 279 da aka sace daga makarantar sakandaren kwana ta Jangebe da ke jihar Zamfara.

Matawalle yace wasu daga cikin tubabbun 'yan bindigan ne suka taimaka masa wurin karbo 'yammatan.

Ya ce gwamnatinsa bata taba baiwa wani tubabben dan bindiga kudi ba sai dai ta koyar da su sana'o'in dogaro da kai.

KU KARANTA: Gara mu yi asarar kayan, 'Yan kasuwan arewa sun yi martani kan hana kudu kayan abinci

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya ce biyan makuden kudaden fansa zai cigaba da habaka ta'addancin garkuwa da mutane, jaridar Daily Trust ta wallafa hakan.

Ya ce: "Lokaci ya sauya gaba daya, akwai takaici tare da bada haushi a lamurran garkuwa da mutane."

A wata takardar da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba shehu ya fitar, yayi kira ga sojoji da 'yan sanda da su bibiya masu garkuwa da mutane har sai sun tabbatar da adalci.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel