Yanzu-Yanzu: An Bayyana ranar da za'a yima shugaba Buhari Da Osibanjo allurar rigakafi

Yanzu-Yanzu: An Bayyana ranar da za'a yima shugaba Buhari Da Osibanjo allurar rigakafi

- Hukumar (NPHCDA), ta fadi ranar da za'a yima shugaba Buhari da mataimakinsa Osibanjo allurar rigakafi bayan isowar allurar najeriya.

- NAFDAC tayi gargadi a kan cewa akwai gurbatattun allurar da suka shigo kasuwa don haka mutane su lura

- Ana sa ran shuwagabannin zasu bayyana a kafar talabijin don a musu kowa ya gani

A ranar Asabar mai zuwa za'a yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa farfesa Yemi Osibanjo allurar rigakafin cutar korona a bainar jama'a.

Matakin yiwa shugaban da mataimakinsa rigakafin a bayyane ya yi daidai saboda kore shakku da wasu mutane kema allurar rigakafin.

Shugaban hukumar kula da lafiya ta kasa NPHCDA, Dr. Faisal shu'aib ne ya bayyana haka a wani zama kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

KARANTA ANAN: Bincike ya fallasa yadda masu hakar gwal ta bayan-fage suke hura wutan rashin tsaro

Zaman ya maida hankali ne a kan matakin da Najeriya ta dauka na rage yaduwar cutar a shekara daya da ta gabata.

Dr Faisal ya kara da cewa:"Za'a yiwa shugaban kasa da mataimakinsa allurar rigakafin Oxford/AstraZeneca ranar Asabar."

Amma sai bayan anyi ma wasu ma'aikatan lafiya kwana daya kafin lokacin.

Yanzu-Yanzu: An Bayyanar ranar da za'a yiwa shugaba Buhari Da Osibanjo allurar rigakafi
Yanzu-Yanzu: An Bayyanar ranar da za'a yiwa shugaba Buhari Da Osibanjo allurar rigakafi Hoto: @NCDCgov
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Kungiyar Ibo ta maidawa ‘Yan Arewa martani, ta ce za mu fara noma abincin da ku ke takama da shi

Faisal ya ce, a wannan rana shima shugaban kwamitin yaki da cutar kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha za'ayi masa rigakafin.

A nashi jawabin, shugaban hukumar kare yaduwar cututtuka ta kasa, Dr Chikwe Iheakwazu, yace da zarar an gwada allurar to komai zai cigaba da tafiya daidai.

A bangarensa, shugabar hukumar (NAFDAC), Prof. Mojisola Adeyeye ta yi kashedi ga mutane cewa akwai gurbatacciyyar allurar rigakafin data fito kasuwa.

Ta kara da cewa "Shiyasa hukumar (NAFDAC) ta maida hankali wajen bincikosu don tabbatar da anyi rigakafin ingantanciya."

"Zamu cigaba da bibiyar allurar har zuwa sanda za'a yiwa wanda ya dace," a cewar ta.

Ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire, shima ya yi gargadi da cewa:

"Najeriya tayi sa'a sosai amma dole mu cigaba da wannan nasarar, mu cigaba da daukar matakai daban-daban, ba maganunguna kadai ba."

"Dole mu kalli allurar a mahanga mai kyau, mu kalleta a matsayin wadda zata chanza mana halin da muke ciki," ministan lafiya ya fada.

A wani labarin kuma Daliban Jangebe sun ce da maigadin makarantarsu aka hada kai wurin sacesu, Matawalle

Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara ya ce 'yammatan Jangebe sun bayyana cewa maigadinsu na makaranta yana daga cikin wadanda aka hada kai dasu aka sacesu.

Ya tabbatar da cewa za a bincika a gane sahihancin zancen kafin a dauka mataki a kansa tare da sauran wadanda aka hada kai dasu.

Matashi mai burin zama babban dan jarida Ahmad Yusuf.

Za'a iya bibiyarsa a kafar sada zumunta wato instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Online view pixel