Kungiyar Ibo ta maidawa ‘Yan Arewa martani, ta ce za mu fara noma abincin da ku ke takama da shi

Kungiyar Ibo ta maidawa ‘Yan Arewa martani, ta ce za mu fara noma abincin da ku ke takama da shi

- Ohanaeze Ndigbo ta yi martani a kan yajin aikin kai abinci zuwa yankin Kudu

- Kungiyar Ibon ta ce matakin nan da aka dauka zai taimakawa Kudancin kasar

- Mutanen Ibo ta bakin Alex Ogbonnia sun ce noma za su fara babu kaukautawa

A ranar Laraba, 3 ga watan Maris, 2021, kungiyar kabilar Ibo, Ohanaeze Ndigbo, ta ce hana shigo da abinci da wasu kungiyoyin Arewa su kayi ba zai taba su ba.

Jaridar Punch ta ce Ohanaeze Ndigbo ta tuna yadda aka yi yakin basasa na Biyafara, inda yankin kasar su ka shafe watanni kusan 30 ba tare da sun samu abinci ba.

Wannan kungiya ta yi magana ne ta bakin mai magana da yawunta, Cif Alex Ogbonnia, wanda ya ce kin kawo masu kayan abinci daga Arewa ba wani abin kuka ba ne.

“A wani bangare, su ne ke zaluntarmu. Su ke auka mana. Arewa ta dade ta na jawo matsaloli ta hanyoyi iri-iri. Da mamaki a ce sun fara zanga-zanga, su na bore.”

KU KARANTA: Buhari: A harbe duk wanda aka gani dauke da AK-47

Ya ce:“Babu abin da su ke kawo wa daga Arewa da babu a Kudu. Babu abin da ba za mu iya nomansa ko mu raina a Kudu ba. Saniyar ce? Doya ce? Ko yalon bello?

Alex Ogbonnia yake cewa: “Kasar kudu ta na da kyau, kuma za ta dauki duk abin da aka shuka.”

A cewar Ogbonnia, hana kawo masu kayan abincin da aka yi, zai bude wa mutanen Ibo kofa ne.

“Mu na jiran saukar ruwan farko ne kawai. Ruwan sama na zuwa, za mu fara noman duk wadannan kayan abincin da ake kawo wa daga Arewa.” Inji Alex Ogbonnia.

KU KARANTA: Gwamnoni Arewa maso gabas sun bada shawarar dauko Sojojin haya

Kungiyar Ibo ta maidawa ‘Yan Arewa martani, ta ce za mu fara noma abincin da ku ke takama da shi
Shugabannin Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Hoto: guardian.ng
Asali: Facebook

Kakakin Ohanaeze Ndigbo ya ce hakan abu ne mai kyau. “Zuwa watan Yuni, Oktoba da Nuwamba, za a ga kayan abinci sun cika yankin Kudancin Najeriya baja-baja.”

“Shekaru uku na Biyafara ba su kashe mu ba, sai a yanzu ne wata daya rak zai kashe mu.”

A jiya ne aka ji cewa kungiyar gamayyar dillalan shanu da kayan masarufi a Najeriya, AUFCDN ta amince ta janye takunkumin hana kai abinci zuwa yankin Kudu.

AUFCDN ta bada wannan sanarwa ne a wata ganawa da ta gudana da wasu gwamnonin jihohi a Abuja a ranar Laraba, inda aka yi zama domin shawo kan lamarin.

Wani shugaban matasan dillalan shanu a Legas, ya ce gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya na cikin wadanda su ke kokarin ganin an kawo karshen takunkumin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel