Makuden kudaden fansa na karfafawa masu garkuwa da mutane guiwa, Buhari

Makuden kudaden fansa na karfafawa masu garkuwa da mutane guiwa, Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kudaden da ake biyan masu garkuwa da mutane yana kara musu karfin guiwa

- Kamar yadda yace, lamarin sace mutane domin karbar kudin fansa abu ne mai matukar takaici a kasar nan

- Shugaban kasan ya bukaci 'yan sanda da sojoji da su bibiyi miyagun mutanen tare da tabbatar da an yi wa jama'a adalci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya ce biyan makuden kudaden fansa zai cigaba da habaka ta'addancin garkuwa da mutane, jaridar Daily Trust ta wallafa hakan.

Ya ce: "Lokaci ya sauya gaba daya, akwai takaici tare da bada haushi a lamurran garkuwa da mutane."

A wata takardar da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba shehu ya fitar, yayi kira ga sojoji da 'yan sanda da su bibiya masu garkuwa da mutane har sai sun tabbatar da adalci.

KU KARANTA: 'Yan bindigan da suka sace mu sun bukaci mu dinga musu addu'a, 'Yammatan Jangebe

Makuden kudaden fansa ne karfafawa masu garkuwa da mutane guiwa, Buhari
Makuden kudaden fansa ne karfafawa masu garkuwa da mutane guiwa, Buhari. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

Ya nuna tsabar murnarsa tare da jin dadinsa bisa ga sakin yaran matan makarantar sakandare da aka sace a jihar Zamfara inda yace: "Ina taya iyalai da jama'ar jihar Zamfara murnar sako wadannan yara da suka firgita."

Buhari wanda sam bai yi farin ciki da mummunan lamarin ba, ya nuna jin dadinsa na yadda lamarin ya kare.

"Garkuwa da mutum mummunan lamari ne ba ga wanda aka sacen ba kadai, hatta iyalansu da dukkanmu baki daya."

Yayi kira ga jama'a da su kara zuba ido ta yadda za a samu bayanan sirri wadanda za su sa a bankado duk wani mugun shirin 'yan bindigan.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun bamu lambobin waya, sun ce za su zo neman aurenmu, 'Yammatan Jangebe

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada cewa babu sasanci da zai shiga tsakaninta da 'yan bindiga duk da hauhawar miyagun ayyukansu a jihar.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya sanar da gidan talabijin na Channels a wata tattaunawa cewa 'yan bindigan da ke kawo hari duk daga jihohi masu makwabtaka ne, don haka babu dalilin sasanci da su.

Ya kara da yin bayanin cewa gwamnatin jihar tare da hadin guiwar ta tarayya suna aiki tukuru domin ganin sun shawo kan hare-haren da suka ta'azzara ballantana a kauyuka.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel