Da ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A Jigawa

Da ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A Jigawa

- Jam'iyar PDP ta kori tsohon dan takarar gwamna a jigawa

- Kwanan baya dan takarar yayi sa'insa da tsohon gwamnan jihar Sule Lamido

- shugaban jam[iyar na jihar Ibrahim babandi ya bayyana haka

Jam'iyyar PDP reshen jihar Jigawa ta kori Aminu Ibrahim, ɗan takarar ta na gwamna a zaɓukan 2015 da 2019 da suka gabata bisa tuhumar sa da cin amanar jam'iyyar.

Wannan mataki dai yana da alaƙa da saɓanin da shi Aminu Ibrahim ɗin ya samu da tsohon gwamnan jahar wato Sule Lamido wanda Aminun yayi wa shugaban ma'aikata a lokacin da yake kan karagar mulki.

Premium times ta ruwaito cewa a ranar Laraba shugaban jam'iyyar PDP na jihar ta jigawa wato Ibrahim Babandi ya bayyana cewa yan majalissun ƙoli na jam'iƴƴar suka yanke hukuncin korar Ibrahim ɗin.

KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: Kungiyar Dilallan Shanu da Kayan Masarufi sun amince da janye takunkumin kai kaya Kudu

"An cimma matsayar daukar wannan mataki ne bayan gano cewa Aminu Ibrahim yayi ma jam'yyar zagon ƙasa tun daga matakin jaha har ya zuwa na kananan hukumomi." Inji Ibrahim Babandi.

Da ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A Jigawa
Da ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A Jigawa Hoto: Guardian.ng
Asali: UGC

KARANTA ANAN: Na Rasa Inda Zansa kaina Saboda Farin Ciki, A Cewar Wani Mahifi Bayan Sako Yan Matan Jengebe

Yace Aminu ya ki ya bayyana don kare kanshi akan tuhumar da ake mishi a gaban kwamitin mutum 7 da jam'iyyar ta kafa.

Sai dai a nashi ɓangaren, Aminu ya bayyana cewa korar da ake iƙrarin an yi mishi aikin banza ne kawai. Yace kwamitin ƙoli na jam'iyyar jahar basu da hurumin kiran shi don amsa wasu tuhume-tuhume.

Ya kuma bayyana cewa Sule Lamido ne matsalar jam'iyyar a jihar Jigawa

Ya bayyana cewa Sule Lamido yaƙi ya fidda kuɗaɗen da jam'iyyar ta ware don gudanar da yakin neman zabukan 2015 da 2019 da suka gabata wanda hakan ya jawo musu faɗuwa.

Yace ya tura ma uwar jam'iyya ta kasa koke kan yadda Sule Lamido ya riƙa nuna wariya da son kai wanda hakan ya jawo sanadin faɗuwar jam'iyyar a wadannan zaɓukan da suka gabata.

Aminu ya ƙara da cewa a shekarar 2015 ba'a saki kuɗaɗen ba sai a ƙurarren lokaci. Hakan ta sake faruwa a shekarar 2019 wanda ya jawo rashin nasarorin jam'iyyar a zabukan.

A wani labarin kuma Wata Kotu Ta Yankewa Wani Mutumi Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Matar da aka aikatawa dan ta wannan aika aika ta bada shaidar duk abinda ya faru

Matashin ya kashe wani jariri dan kimanin shekaru biyu kacal

Ahmad Yusuf ma'aikacin legit.ng ne da keson aikin jarida. Yayi karatu a KUST wudil.

Za'a iya tuntubarsa a shafin facebook facebook.com/ahmed.yusuf.dabai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel