Da dumi-dumi: Gwamnati ta amince da biyan N797.2bn na aikin hanyar Abuja-Kaduna-Kano

Da dumi-dumi: Gwamnati ta amince da biyan N797.2bn na aikin hanyar Abuja-Kaduna-Kano

- Gwamnatin tarayya ta amince da biyan makudan kudade wajen kaddamar da aikin wasu hanyoyi

- Gwamnatin ta amince da sauya fasalin aikin gyara na hanyoyin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano

- Ana sa ran kammala wasu hanyoyin an ba da dadewa, ciki har da hanyar Kaduna zuwa Zariya

Majalisar zartarwa ta tarayya, (FEC) a ranar Laraba ta amince da kashe sama da naira biliyan 797.2 don aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da yake jawabi ga masu aiko da rahotanni daga fadar gwamnati a karshen mako na taron FEC a fadar Villa dake Abuja, Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya ce Majalisar ta amince da sauya fasalin yin aikin.

A cewarsa, titin, wanda har yanzu ana kan aikin gyara shi, yanzu za a sake gina shi gaba daya, don haka an canza kudin da ake amfani da shi na aikin daga Naira biliyan 155 zuwa biliyan 797.2.

KU KARANTA: Makinde: Ba za mu bada filayen kiwo ga makiyaya kyauta ba, dole su biya

Da dumi-dumi: Gwamnati ta amince da biyan N797.2bn na aikin hanyar Abuja-Kaduna-Kano
Da dumi-dumi: Gwamnati ta amince da biyan N797.2bn na aikin hanyar Abuja-Kaduna-Kano Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya lissafa hanyoyin da aka gyara, kuma nan bada dadewa ba za a kaddamar dasu, hanyoyin sun hada da Benin zuwa Asaba, Abuja zuwa Lokoja da Kano zuwa Katsina,

Sai kuma daga Onitsha zuwa Aba, Sagamu zuwa Benin, Kano zuwa Maiduguri, Enugu zuwa Port Harcourt, Ilorin zuwa Jebba da Lagos zuwa Badagry .

Da aka tambaye shi ainihin lokacin da za a kammala da hanyar, Fashola ya ce: “To dai, muna ma'amala da hanyoyi ne kimanin kilomita 375. Don haka za a kammala su daki-daki ne.

“Don haka matakin farko shi ne bangaren Kaduna zwa Zariya, wanda yake kilomita 74 da zai kasance a cikin kwata hudu na shekarar 2022.

"Mataki na gaba bangaren Zariya zuwa Kano, wanda yake kilomita 137, ya kamata ya zama a kwata daya na 2023. Sai kuma zango na karshe zai kasance bangaren Abuja zuwa Kaduna wanda ya kamata ya kasance a kwata na biyu na 2023."

K KARANTA: APC ba zata taba iya cire 'yan Najeriya daga kangin da suke ciki ba, in ji Saraki

A wani labarin, Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bukaci masu yi wa sabon shugaban da aka nada, Abdulrasheed Bawa, fatan alheri da su daina biyan kudi don taya shi murna, The Nation ta ruwaito.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ta Wilson Uwujaren ya fitar a shafin Twitter @OfficialEFCC, EFCC ta ce dukiyar da aka kashe kan sakonnin taya murnar za a iya kaiwa ga yin abubuwan da suka dace, kamar tallafawa 'yan gudun hijira.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel