Gwamna Inuwa Yahaya Yayi Waje Da Wasu kwamishinonin sa, Yayi Ma Wasu Kwaskwarima

Gwamna Inuwa Yahaya Yayi Waje Da Wasu kwamishinonin sa, Yayi Ma Wasu Kwaskwarima

- Gwamnatin Gombe Ta sallami wasu kwamishinoninta guda uku

- Bayan haka gwamnan yayi wa wasu ma'aikatun jihar kwaskwarima

-. Inuwa Yahaya yayi wa tsaffin kwamishinonin nasa fatan alkhairy da kuma godiya akan kwazon da suka Nuna lokacin aikin su.

Gwamnan jihar Gombe dake arewa maso yammacin kasar nan Inuwa Yahaya ya sallami wasu Kwamishanoninsa guda 3, ya kuma chanja ma wasu wurin aiki.

TheNation ta ruwaito cewa, wadanda abun yashafa sun hada da; Alhassan Ibrahim Kwami na ma'aikatar Labarai da al'adu, Dr. Ahmed Muhammed Gana na ma'aikatar lafiya, da kuma Mela Audu Nunghe (SAN) na ma'aikatar ayyuka na musamman.

KARANTA ANA: Rundunar Najeriya ta yi asara, Sojojin kasa fiye da 380 sun ajiye aikinsu, sun yi gaba a shekara 1

A sanarwar da sakataren gwamnatin jihar Prof. Abubakar Njodi, ya fitar, yace gyaran hukumomin gwamnati na daga cikin kokarin da suke yi don kara karfafa ayyukan gwamnati da Yahaya keyi.

Gwamna Inuwa Yahaya Yayi Waje Da Wasu Comishinonin sa, Yayi Ma Wasu Kwaskwarima
Gwamna Inuwa Yahaya Yayi Waje Da Wasu Comishinonin sa, Yayi Ma Wasu Kwaskwarima
Asali: Facebook

KARANTA ANAN: Abinda yasa muke kai yara karatu kasashen ketare, Kwankwasiyya

Wadanda akayi ma kwaskwarima sun hada da; Muhammen Danladi Adamu daga ma'aikatar kasa zuwa ma'aikatar bincike da raya karkara, Dr. Habu Dahiru daga ma'aikatar ilimi zuwa ma'aikatar lafiya, da kuma Usman Jafun Biri daga Ma'aikatar Raya karakara zuwa ma'aikatar kasa.

Sauran sun hada da; Julius Ishaya daga ma'aikar Matasa zuwa ma'aikatar Labarai da al'adu, Dauda Batari Zambuk daga ma'aikatar tsaro da bada horo ta cikin gida zuwa ta ilimi, da kuma Adamu Dishi Kupto daga ma'aikatar Gidaje zuwa ta tsaron Cikin Gida.

Gwaman ya yaba da kwazon tsaffin yan majalisar tasu wanda lamarin ya shafa a lokacin aikinsu.

A wani labarin kuma Shugaban kasa Muhammad Buhari, a ranar Talata, ya bada umurnin kaddamar da yaki kan bata gari a Nigeria

Shugaban ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen masu garkuwa, yan bindiga da yan ta'adda da ke adabar kasar.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan shima ya bukaci shugabannin sojoji su tunkari yan bindigan da ke cigaba da kai wa jama'a hari tare da yi wa tsaron kasar barazana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel