Buhari ya bada umurnin ƙaddamar da yaƙi kan ƴan bindiga, masu garkuwa da ƴan ta'adda

Buhari ya bada umurnin ƙaddamar da yaƙi kan ƴan bindiga, masu garkuwa da ƴan ta'adda

- Shugaban kasa Muhammad Buhari, a ranar Talata, ya bada umurnin kaddamar da yaki kan bata gari a Nigeria

- Shugaban ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen masu garkuwa, yan bindiga da yan ta'adda da ke adabar kasar

- Buhari ya zaburar da shugabannin sojoji da sauran hukumomin tsaro su kawo karshen bata garin da ke neman yi wa tsaron kasar barazana

Kwamitin Tsaro na Kasa a taronta na ranar Talata ta yanke shawarar cewa lokaci ya yi da za a dauki kwakwarar mataki a kan masu garkuwa da mutane da yan bindiga da ke adabar kasar nan, rahoton The Nation.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin a kaddamar da yaki kan yan bindiga da masu garkuwa da mutane da yan ta'adda.

Buhari ya bada umurnin a ragargaji 'yan bindiga, masu garkuwa da yan ta'adda
Buhari ya bada umurnin a ragargaji 'yan bindiga, masu garkuwa da yan ta'adda. Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan shima ya bukaci shugabannin sojoji su tunkari yan bindigan da ke cigaba da kai wa jama'a hari tare da yi wa tsaron kasar barazana.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe yayan Sanata Suswam da hadiminsa a Benue

Lawan ya yi wannan jawabin ne bayan tattance shugabannin sojojin da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada.

Mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, NSA, Babagana Monguna, wanda ya sanar da umurnin shugaban kasar bayan taron, ya kuma ce shugaban kasar ya bada umurnin hana jiragen sama shawagi a sararin samaniyar jihar Zamfara.

Ya ce shugaban kasar ya umurci shugabannin sojojin su kwato dukkan garuruwan da yan ta'adda, yan bindiga da masu garkuwa suka mamaye a sassan kasar.

KU KARANTA: Kuma dai, Ƴan bindiga sun sace ɗalibai 3 a jihar Katsina

Har wa yau shugaban kasar ya bada umurnin hukumomin tsaro da na leken asiri su bincike duk mutanen da suke zargi da tada tsaye a kasar.

Ya ce, "Akwai mutane da dama da muke sa ido a kansu, za mu bi sahunsu, za mu binciko su sannan za su fuskanci doka.

"Za a yi musu shari'a kuma za su zama darasi ga wasu, duk wanda ke tunanin zai yi amfani da wannan halin da muke ciki don yi wa gwamnati zagon kasa ya sake tunani," in ji shi.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel