Rundunar Najeriya ta yi asara, Sojojin kasa fiye da 380 sun ajiye aikinsu, sun yi gaba a shekara 1
- Kwamitin sojojin kasa ya yi bincike game da barin aiki da jami’ai su ke yi
- A karshen shekarar bara kawai, an samu sojoji 380 da su ka ajiye aikinsu
- Mafi yawan jami’an na tsere wa ne saboda sha’awar aikin ya fita a ransu
Kwamitin harkar sojojin kasa a majalisar wakilan tarayya ya ce binciken da ya yi, ya nuna sojoji 386 suka ajiye aiki don ganin damarsu a shekarar 2020.
Jaridar Daily Trust ta rahoto kwamitin ya na cewa wadannan sojoji har 386 sun bar aiki ne don gashin kansu, ko kuma larurar rashin lafiya da sauransu.
Shugaban wannan kwamiti, Hon. Abdulrazaq Namdaz, ya bayyana cewa an yi asarar wadannan jami’an sojoji ne a watannin karshen shekarar da ta gabata.
Da yake gabatar da binciken da su ka yi a gaban majalisa a ranar Talata, Abdulrazaq Namdaz ya bada cikakken bayanin yadda aka rasa wadannan sojojin.
KU KARANTA: Sojoji da ‘Yan Sanda sun yi nasarar kashe 'Yan bindigan Katsina
Honarabul Namdaz ya ce sojoji 356 sun yi sallama da gidan sojan ne bayan sha’awar aikin ya fita a ransu.
Bayan haka akwai jami’ai 24 da su ka ajiye aikinsu, bayan sun samu sarautar gargajiya a gida. Sannan kuma an sallami sojoji shida saboda rashin lafiya.
Binciken ya nuna a shekaru biyar da su ka wuce, sojoji 6,752 aka sallama daga aiki. A cikin wannan lokacin, an dauki jami’ai 25, 655 a gidan sojan kasan.
“Rashin son aikin ne babban dalilin da yake jawo wasu sojoji su ke ajiye aiki a gidan soja.”
KU KARANTA: NDLEA ta sa damarar yaki da masu safarar kwayoyi - Janar Marwa
Kamar yadda ‘yan majalisar su ka bayyana, jami’an su kan ajiye aiki ne bayan sun shiga filin daga, sun ga yadda ake gwabza wa da mayakan Boko Haram.
A kwanakin bayan nan ne aka ji cewa sabon shugaban hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya ziyarci wasu rundunonin sojoji da ke jihar Borno.
Shugaban sojojin kasan ya samu rakiyar jami’ai na musamman daga tawagar Operation Lafiya Dole da runduna ta 7 zuwa hedikwatar rundunar da ke Borno.
Janar I. Attahiru ya karbi aiki daga hannun Laftana-Janar Tukur Buratai ne a karshen Junairu.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng