Ni dan kai sako ne, in ji mutumin da aka kama da kawunan mutane 2 a Akure

Ni dan kai sako ne, in ji mutumin da aka kama da kawunan mutane 2 a Akure

- Hukumar NDLEA a jihar Ondo ta damke wani mutum mai suna Saka Hassan dauke da kawunan mutane biyu

- Sai dai Saka ya ce an aike shi ne domin ya kai wa wani sakon daga garin Lokoja ta jihar Kogi

- Ya ce bai san wanda ya aikensa ba illa dai an bashi lambar wayar wanda zai karbi sakon idan ya kai

Wani dan shekara 30 mai suna Saka Hassan, wanda aka kama da kawunan mutane biyu, ya ce zai kai su wurin wani ne a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Hassan ya ce yana tuka motar haya kuma ya na hanyar Akure-Okene tsawon shekaru 15 da suka gabata, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya ce an ba shi kwali da ke dauke da kawunan mutanen a Lokoja ne don ya kai wa wani a Akure.

Ni dan kai sako ne, in ji mutumin da aka kama da kawunan mutane 2 a Akure
Ni dan kai sako ne, in ji mutumin da aka kama da kawunan mutane 2 a Akure Hoto: PM News
Asali: UGC

Wanda ake zargin ya ce bai san wanda aka karbi kayan a hannunsa ba domin shi yana da lambar wayar mai karban sakon ne kawai, yana mai cewa mai shi ya ajiye kwalin ne kawai sannan ya tafi nan take.

KU KARANTA KUMA: Afenifere, Igboho da OPC sun shirya gangamin hannun riga da naman shanu

Jami'an hukumar hana fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ne suka kama Hassan din akan hanyar Owo-Akure a jihar Ondo.

An rufe kawunan biyu a cikin kwali mai ruwan kasa.

Kwamandan NDLEA na jihar, Mista Haruna Gagara, ya ce mutanensa da ke sintiri a kan hanyar Owo - Akure sun tare wata motar Nissan Sunny kalar ruwan toka mai lamba KOGI: LKJ 135 BF sannan suka sami kawunan mutum biyu.

Ya ce za a mika wanda ake zargin ga ‘yan sanda don yi masa hukunci.

A wani labarin, koda dai gwamnatin Neja ba ta fitar da sanarwa a hukumance da ke sanar da cafke masu satar mutanen da suka sace daliban Kagara ba, amma hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta damke wasu bindigogi daga hannun miyagu a jihar.

A cewar shugaban rundunar ta NDLEA a Neja, Aloye Isaac Oludare, an kama wadanda ake zargin, Danjuma Auta da Daniel Danrang a ranar Litinin, 1 ga Maris, kan hanyar Kontagora-Zuru, TVC News ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Kano: 'Yan Hisbah sun damke matasa 2 akan zargin tura wa matar aure bidiyon shahanci

Oludare ya bayyana cewa an kama dillalan bindigogin ne da bindigogin AK 47 guda 12 da kuma kananan bindigogi guda 15.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng