Kano: 'Yan Hisbah sun damke matasa 2 akan zargin tura wa matar aure bidiyon shahanci

Kano: 'Yan Hisbah sun damke matasa 2 akan zargin tura wa matar aure bidiyon shahanci

- Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu matasa biyu bisa zargin tura wa wata matar aure sokonni wadanda suke dauke da batsa

- Kakakin hukumar, Lawan Ibrahim, ya tabbatar da hakan ta wata takarda, wacce ya tabbatar da cewa matar ce ta kai musu korafi

- A cewar Lawan, kamar yadda matar tayi korafi, bata gane wadanda suke tura mata sakonnin ba da ke dauke da batsa a wayarta

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu matasa biyu bisa zargin tura wa wata matar aure sakonni na batsa.

A wata takarda wacce kakakin hukumar, Lawan Ibrahim, ya gabatar, ya bayyana yadda suka samu nasarar bin diddiki wurin gano matasan da kuma kama su bayan tayi korafi ga hukumar.

A cewar Lawan, ita da kanta tayi korafi akan yadda wasu wadanda bata sani ba suke tura mata sakonni dauke da batsa ta wayarta, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun bamu lambobin waya, sun ce za su zo neman aurenmu, 'Yammatan Jangebe

Kano: 'Yan Hisbah sun damke matasa 2 a kan zargin turawa matar aure bidiyon batsa
Kano: 'Yan Hisbah sun damke matasa 2 a kan zargin turawa matar aure bidiyon batsa. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

"Hukumar ta amshi lambobin wayar daga hannunta inda tayi bincike har ta kama matasan a Unguwa Uku dake karamar hukumar Tarauni. Matasa ne wadanda basu wuce shekaru 20 zuwa 21 ba.

"Mun gayyaci iyayensu don tattaunawa da su kuma sun mayar da hankulansu garesu don gudun cigaba da tabarbarewar tarbiyyarsu," kamar yadda takardar ta shaida.

Lawan ya shawarci iyaye da su guji siyawa yaransu tsadaddun wayoyi kuma su kula da yadda yaransu suke tafiyar da rayuwarsu da kuma mugayen abokai da kawaye.

KU KARANTA: Da duminsa: Mayakan ISWAP da sojin Najeriya ana musayar wuta a Dikwa, Borno

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada cewa babu sasanci da zai shiga tsakaninta da 'yan bindiga duk da hauhawar miyagun ayyukansu a jihar.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya sanar da gidan talabijin na Channels a wata tattaunawa cewa 'yan bindigan da ke kawo hari duk daga jihohi masu makwabtaka ne, don haka babu dalilin sasanci da su.

Ya kara da yin bayanin cewa gwamnatin jihar tare da hadin guiwar ta tarayya suna aiki tukuru domin ganin sun shawo kan hare-haren da suka ta'azzara ballantana a kauyuka.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel