Kada kubari a yaudare ku, Gwamnan Bauchi yayi kira ga al'ummar Mazabar Dogara

Kada kubari a yaudare ku, Gwamnan Bauchi yayi kira ga al'ummar Mazabar Dogara

- Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi yayi kira ga al'umma da su bashi hadin kai.

- A baya bayannan ne gwamnan yakai ziyara don duba wasu ayyuka a mazabar tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu dogara

- Tawagar Gwamnan Bauchi Tayi Hatsara, wasu yan sanda sun rasa rayukan su

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammed yayi kira ga mutanen mazabar tarayya ta Dass/Bogoro/Tafawa, mazabar da tsohon kakakin majilisar wakilai Yakubu Dogara ke wakilta a majalisar wakilai, da su nuna masa goyon baya don ya kawo chanji a jihar.

Da yake bayyana haka lokacin da yaje duba ayyukan da akeyi a kananan hukumomin Tafawa Balewa da Bogoro yace "ya kamata kusani cewa da ni daku duk daya muke. Dukkan mu daga karamar kabila muke a jihar. Don haka ya zama wajibi mu hada kan mu domin kawo cigaba."

A lokacin da Gwamna Muhammed yaje duba ayyukan wasu hanyoyin a karamar hukumar Bogoro, Mahaifar tsohon Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya tabbatar musu da cewa gwamnatinsa baza ta basu kunya ba.

DUBA NAN: Wike ya sasanta gwamnan jihar Benue da na Bauchi kan batun makiyaya

Kada kubari a yaudare ku, Gwamnan Bauchi yayi kira ga al'ummar Mazabar Dogara.
Kada kubari a yaudare ku, Gwamnan Bauchi yayi kira ga al'ummar Mazabar Dogara. Credit: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

KU KARANTA: Munguno: Muna da rahotannin sirri na wadanda ke cin gajiyar rashin tsaro

A bangare guda, Gwamnan Benue Samuel Ortom da takwaransa na jihar Bauchi Bala Mohammed a ranar Talata sun rungumi juna bayan sulhun da Gwamnan Ribas Nyesom Wike ya shirya, The Nation ta ruwaito.

Gwamnonin biyu sun yi rikici a bainar jama'a game da kashe-kashen makiyaya a fadin kasar.

Bala Mohammed ya kare makiyaya kan daukar bindigogin AK-47, yana mai cewa suna yin hakan ne domin kare kansu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel