Aiki ga mai kare ka: An yi ram da kwayoyin Biliyan 60 bayan Buhari ya nada Buba Marwa a NDLEA

Aiki ga mai kare ka: An yi ram da kwayoyin Biliyan 60 bayan Buhari ya nada Buba Marwa a NDLEA

- Kwanakin baya aka nada Buba Marwa a matsayin sabon Shugaban NDLEA

- A makonni shida rak, NDLEA ta cafke kwayoyi na sama da Naira Biliyan 60

- Buba Marwa ya yi kira ga jama'a su taimaka masu wajen yakar shaye-shaye

Hukumar NDLEA mai yaki da safarar miyagun kwayoyii a Najeriya ta karbe kwayoyi na sama da Naira biliyan 60 a fadin Najeriya a makonni shida.

A ranar Litinin, 1 ga watan Maris, 2021, NDLEA ta bayyana cewa ta ci wannan nasara ne bayan Janar Mohamed Buba Marwa ya zama shugabanta.

Janar Mohamed Buba Marwa (rtd) ya yi kira ga shugabannin addini su bada gudumuwa wajen yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi a kasar nan.

A wani jawabi da ya fito ta bakin darektan yada labarai da wayar da kai na NDLEA, Femi Babafemi, hukumar ta bukaci malamai su taimaka mata.

KU KARANTA: Yadda za a bi a kama Shugaban Boko Haram, Shekau - Fasto

Shugaban NDLEA ya yi wannan bayani ne bayan gwamna Umoru Ahmadu Fintiri ya kawo masa ziyara zuwa babban ofishin hukumar na jihar Adamawa.

Da yake jawabi a ofishin NDLEA, Umoru Ahmadu Fintiri, ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnati a kowane mataki ta dafa wa hukumar ta NDLEA.

Gwamna Ahmadu Fintiri yake cewa dole a yaki miyagun kwayoyi kafin su kai ga hallaka Najeriya.

A jawabinsa, Mohamed Buba Marwa ya ce kamen da su ka yi na kwayoyin da darajarsu ta haura Naira biliyan 60, gagarumar nasara ce da aka samu a karkashinsa.

Aiki ga mai kare ka: An yi ram da kwayoyin Biliyan 60 bayan Buhari ya nada Buba Marwa a NDLEA
Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa mai ritaya Hoto: thisdaylive.com
Source: UGC

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sace ‘Dan kasuwa a Sokoto

“Ton 230 na tabar wiwi da aka kama a jihar Edo, shi ne babban kamen da aka taba yi a tarihin NDLEA, an samu wannan nasara ne saboda aikin jami’anmu.”

Dazu ne ku ka ji cewa shugaban kasa ya zabi Dr. Halilu Shaba Ahmad a matsayin shugaban NASRDA mai kula da bincike da nazari a kan fasahar sama jannati.

Dr. Shaba Ahmad zai jagoranci Hukumar NASRDA idan Majalisar dattawa ta tantance shi.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya karanto wasikar shugaban kasar a ranar Talata, 2 ga watan Maris, 2021, inda aka ji ya nada Halilu Shaba Ahmad.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel