Atiku ya gargadi Buhari: Kada ka yarda a sake sace dalibai a kasar nan

Atiku ya gargadi Buhari: Kada ka yarda a sake sace dalibai a kasar nan

- Tsohon matamakin shugaban kasar Najeriya ya gargadi gwamnati kan sace-sacen dalibai

- Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bukaci gwamnati da ta maida hankali kan tsaron yara

- Hakazalika ya taya iyaye murnan sakin 'ya'yansu da akayi, ya kuma yi adduar Allah ya tsare

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya gargadi Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da ta tabbatar da cewa satar yaran makaranta bai sake faruwa ba, PM News ra ruwaito.

Atiku ya mayar da martani ne kan sakin 'yan mata 279 na makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe, jihar Zamfara a ranar Talata.

Ya ce a matsayinsa na uba, ya yi matukar farin ciki da sakin daliban kuma ya yi wa danginsu murna.

Atiku ya ce yana addu’ar sauran ‘yan matan ma a sako su nan ba da jimawa ba.

KU KARANTA: COVID-19: A fara yiwa jami'an gwamnati rigakafin kafin talakawa, in ji Tomori

Atiku ya gargadi Buhari: Kada ka yarda a sake sace dalibai a kasar nan
Atiku ya gargadi Buhari: Kada ka yarda a sake sace dalibai a kasar nan Hoto: Gist Flash
Asali: UGC

“A matsayina na uba, na yi farin ciki da sakin dalibai 279 na GGSS Jangebe. Duk da ina murna ga dangin wadanda aka sake, ina fata da addu'a cewa a sako sauran 'yan matan nan ba da jimawa kuma su kasance tare da danginsu da masu kaunarsu.

“Babu wani dalibi, mahaifi ko dan kasa da ya kamata ya sake shiga wannan mawuyacin hali. Ina taya gwamnatin jihar Zamfara da duk wadanda suka yi aiki cikin hadin kai don ganin an dawo da wadannan 'yan mata lami lafiya,” inji shi.

Atiku ya ce yana da yakinin cewa gwamnati za ta tabbatar da sakin sauran wadanda abin ya shafa, amma ya ce babban aiki shi ne gwamnatin Buhari ta tabbatar da cewa irin wannan bai sake faruwa ba.

“Ina da yakinin cewa gwamnati za ta tabbatar da sakin sauran wadanda abin ya shafa.

"Babban aikin shi ne tabbatar da cewa irin wadannan abubuwan ba su sake faruwa ba, kuma hakan wata manufa ce da ya kamata gwamnatin tarayya ta jagoranta," in ji shi.

KU KARANTA: Yanzun nan: Allurar rigakafin kwayar cutar COVID-19 ta iso Najeriya

A wani labarin, ‘Yan mata 317 da aka sace daga Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe, a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya, sun dawo, in ji Gwamnan Jihar.

Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita cikin daren Talata, 2 ga Maris, 2021. A jawabinsa, ya bayyana irin jajircewan da suka yi domin ganin cewa an sako wadannan dalibai 317.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: