Bayan wata uku da sace su: Na ga mahaifina da yayata a wurin yan bindiga, dalibar Jangebe da aka sako
- Habiba, daya daga cikin daliban Jangebe da aka sako ta bayyana cewa ta ga mahaifinta da yayarta da aka sace watanni uku a wajen yan bindigar da suka yi garkuwa da su
- Ta bayyana cewa mahaifin nata na cikin mawuyacin hali domin yana shan azaba a wajen yan ta'addan saboda rashin biyan kudin fansa
- Sai dai kuma ta ce mahaifin nata ya gargade ta a kan kada ta nuna ta san shi saboda kada maharan su cutar da su
Daya daga cikin yan matan makarantar GGSS Jangebe da aka sako, ta bayyana cewa ta hadu da mahaifinta da yayarta a wurin yan bindigar da suka sace su.
Dalibar mai shekaru 14 ta bayyana cewa mahaifin nata wanda ya shafe tsawon watanni uku a wurin maharan, na cikin hatsari babba kuma ya gargade ta a kan kar ta nuna ta san shi, idan ba haka ba yan bindigar za su halaka shi.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa cikin kuka, yarinyar ta bayyana mata yadda haduwar tasu ta kasance da kuma irin nau’in azabar da yan bindigar ke gana wa mahaifin nata a kan idanunta.
KU KARANTA KUMA: Yan ta’adda sun sake kai hari, sun kashe mutane 10 a Kaduna, sun sace 3 a jihar Neja
Ta kuma bayyana cewa akwai yiwuwar su kashe shi.
Ya ce:
“Yan bindiga sun rufe masa fuska, bayan an kwance abunda aka rufe masa fuskar da shi, sai ya hango ni a cikin dalibai ya kira sunana.
“Ya ce Habiba ke ce? Na amsa na ce ni ce. Sai ya kara tambayata mutanen gida Suna lafiya?
“Sai kuma ya gargade ni da kada na sake na nuna cewar na san shi ko yayata, idan ba haka ba duk za su kashe mu.
“Da yan makarantarmu suka gane cewa mahaifina ne Sai suka ba ni shawarar bin umurninsa.”
Ta bayyana cewa an sace mahaifinta da yayar tata ne a wani hari da aka kai gidansu watanni uku da suka gabata.
“A harin ne aka kashe kawuna, kuma duk kokarin da aka yi din ceto su ya ci tura saboda makudan kudaden da aka bukata na fansa.
“Sun raunata shi sosai ta hanyar sara sa da adda da kuma dukan da yake sha.
“A duk lokacin da na ga yan bindigar na dukan shi sai na yi kuka saboda tashin hankalin da muke ciki.
KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: 'Yan Boko Haram sun ƙwace Dikwa da dubban mutane cikin garin
“Kuma maharan sun ce za su kashe su idan ba a biya kudin fansa ba,” cewarta.
A gefe guda, Ɗaya daga cikin daliban makarantar sakandare ta mata na Jangeɓe da aka sace makon da ya gabata, Hafsat Anka, ta ce masu garkuwar sunyi barazanar za su kashe su, su soya su sannan su cinye su idan suka yi rashin ji, News Wire ta ruwaito.
Hafsat, yayin da ta ke bayyana wa kamfanin Dilancin Labarai NAN halin da suka shiga ta ce sun yi tafiya na awanni bayan sace su kafin su kai wurin da aka ajiye su.
Ta magantu ne a gidan gwamnati da ke Gusau bayan an sako su kamar yadda News Wire ta ruwaito.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng