Yan ta’adda sun sake kai hari, sun kashe mutane 10 a Kaduna, sun sace 3 a jihar Neja

Yan ta’adda sun sake kai hari, sun kashe mutane 10 a Kaduna, sun sace 3 a jihar Neja

- Yan bindiga sun kashe wasu mutane a Kaduna yayinda suka kashe wasu jihar Neja

- Hakazalika, an banka wa gidaje 10, babura biyu da buhuhunan citta guda 50 wuta

- A halin da ake ciki, ana zargi mayakan Fulani a Kakwa da ke masarautar Atyap a Zangon da kai harin

A wani labari mai karya zuciya, wasu bayin Allah sun sake rasa ransu a hannun yan ta’adda a Najeriya.

A wannan karon, yan bindigan sun kashe kimanin mutane 10 a Zangon Kataf da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan.

Yan ta’adda sun sake kai hari, sun kashe mutane 10 a Kaduna, sun sace 3 a jihar Neja
Yan ta’adda sun sake kai hari, sun kashe mutane 10 a Kaduna, sun sace 3 a jihar Neja Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai hari garuruwa uku a Neja cikin sa’o’i biyu, sun kashe 3 da yin garkuwa da wasu da dama

A cewar jaridar The Guardian, harin Zangon Kataf, kauyen Kurmin Gandu ya yi sanadiyar rasa tan mutum biyar masu suna, Ishaya Aboi, Regina Ishaya, Goodluck Dauda, Joseph Adamu da Hassan Joseph.

Da yake ci gaba, ya bayyana cewa yan bindigar sun cinna wa gidaje 10, babura biyu da buhuhunan citta 50 wuta.

Aruwan ya kuma kara da cewa an fara bincike da aikin ceto a yankunan da abun ya shafa yayinda aka dauki masu rauni zuwa asibiti don karbar magani.

A halin da ake ciki, kungiyar mutan Kudancin Kaduna (SOKAPU) sun zargi mayakan Fulani a Kakwa da ke masarautar Ayap a Zangon Kataf da kai harin.

An yi garkuwa da mutum 3 a Neja

Hakazalika, a jihar Neja, yan bindiga sun sace mutum uku - mace daya da maza biyu a garin Katcha.

Yan bindigar sun farma masu shaguna ne, musamman masu wajen shan kayan maye, a wajen garin, bayan gidan shugaban yan sanda (DPO).

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun yi barazanar kashe mu, su soya namar mu su cinye, Ɗalibar Jangebe

An tattaro cewa yan bindigan sun shafe sa’o’i uku suna aiki ba tare da tangarda ba kafin suka tafi da mutanen.

A wani labarin, Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, a ranar Talata ya bayyana cewa yayinda suke kokarin ganin cewa an saki daliban GGSS Jangebe da aka sace, wasu na kokarin baiwa yan bindigan kudi don kada su saki daliban.

Matawalle ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga Daliban da safiyar Talata.

Ya ce nan ba da dadewa ba zai bayyana ummul haba'isin sace daliban da kuma yayi kira ga masu ingiza yan bindiga su bi a hankali.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel