Wasu sun yiwa yan bindiga tayin kudi don kada su saki daliban Jangebe, Inji Matawalle

Wasu sun yiwa yan bindiga tayin kudi don kada su saki daliban Jangebe, Inji Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, a ranar Talata ya bayyana cewa yayinda suke kokarin ganin cewa an saki daliban GGSS Jangebe da aka sace, wasu na kokarin baiwa yan bindigan kudi don kada su saki daliban.

Matawalle ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga Daliban da safiyar Talata.

Ya ce nan ba da dadewa ba zai bayyana ummul haba'isin sace daliban da kuma yayi kira ga masu ingiza yan bindiga su bi a hankali.

Ya kara da cewa ya fadawa jami'an tsaro irinsu yan sanda, DSS da Soji kuma sun kaddamar da bincike kan lamarin.

"Kwana hudu ban yi bacci ba. Mun yi kokari matuka don tabbatar da yan matan nan sun dawo gida wajen iyayensu," Yace.

"Muna amfani da karfin Soja da na sulhu, kuma na sulhun na yi mana aiki. Idan ba haka ba, da bamu samu nasarar ceto yaran nan ba."

Ya bayyana cewa daliban da aka sace 279 ne sabanin 317 da aka ruwaito.

Wasu sun biya yan bindiga kudi don kada su saki daliban Jangebe, Inji Matawalle
Wasu sun biya yan bindiga kudi don kada su saki daliban Jangebe, Inji Matawalle Credit: TVC
Source: Facebook

Source: Legit.ng

Online view pixel