Kagara: 'Yan bindiga basu tausayi ko tsoro, sun ce alkawarinsu gwamnati ta karya, Hauwa

Kagara: 'Yan bindiga basu tausayi ko tsoro, sun ce alkawarinsu gwamnati ta karya, Hauwa

- Hauwa Abdulsalam, daya daga cikin 'yan Kagara da suka kubuta ta bada labarin tattaunawarta da 'yan bindiga

- Ta kwatanta su da mutane marasa tsoro da imani wadanda suka ce gwamnati ta karya musu alkawari

- Hauwa ta ce Kachalla Ali, shugaban 'yan bindigan ya yi barazanar yanka su matukar ba a cika sharadi ba

Daya daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su aka sako na kwalejin kimiyya da ke Kagara a jihar Neja ta bada labarin abinda ta fuskanta yayin da suke hannun 'yan bindiga.

Hauwa Abdulsalam wacce ta kwatanta 'yan bindigan da marasa tausayi da tsoro, ta bayyana cewa shugaban 'yan bindigan, Kachalla Ali ya rantse cewa zai fara kashe mazan ciki kafin su kai kan matan idan ba a cika sharadin da suka bada ba.

Ta kara da bayyana cewa 'yan bindiga sun zargi shugabanni da karya musu alkawarin da suka dauka yayin zabe, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

KU KARANTA: Caccakar Buhari: DSS ta cafke hadimin Ganduje, Dawisu, bayan yace APC ta gaza

Kagara: 'Yan bindiga basu tausayi ko tsoro, sun ce alkawarinsu gwamnati ta karya, Hauwa
Kagara: 'Yan bindiga basu tausayi ko tsoro, sun ce alkawarinsu gwamnati ta karya, Hauwa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Hauwa wacce ta tambaya 'yan bindigan abinda gwamnati ta yi musu alkawari, ta ce sun tabbatar mata da cewa gwamnati ta ce za ta samar musu da gidaje, asibitoci kuma ta dinga biyan su albashi.

Dalibar wacce tace 'yan gidansu sun fi yawa a cikin wadanda aka sace, ta mika godiyarta ga Allah da ya bata tsawon kwana.

KU KARANTA: Iyayen yara sun ragargaza makarantar da aka sace dalibai mata a Zamfara, Malami

A wani labari na daban, daga bisani 'yan bindiga sun saki 'yan makarantar kwalejin kimiyya ta gwamnati tare da malamansu da aka sace.

An sako su a sa'o'in farko na ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairun 2021, jaridar Vanguard ta wallafa.

Majiya mai karfi ta sanar da cewa a halin yanzu wadanda aka sace suna kan hanyarsu ta zuwa Minna kuma nan da sa'o'i kadan za su isa babban birnin.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel