Ban taba karbar ko sisi ba a shekaru 8 da nayi a gwamnan jiha, Tsohon gwamna
- Tsohon gwamnan jihar Osun kuma ministan Buhari ya ce bai taba karbar ko sisi ba a matsayin albashi lokacin yana gwamna
- Ogbeni Rauf Aregbesola ya musanta labarin da ke yawo cewa ya samu albashin watanni 96 a sirrance kafin karewar wa'adinsa
- A cewarsa, gwamnati ta samar masa da wurin zama, abinci, sufuri da sauransu, don haka baya bukatar albashi
Tsohon gwamnan jihar Osun kuma ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola a ranakun karshen mako ya musanta labarin da ke yawo na cewa ya samu albashinsa na watanni 96 a sirrance a lokacin da yayi shugabancin jihar.
Ya kwatanta rahoton da labarin kanzon kurege wanda aka hada shi domin zubar da nagartar Ogbeni Rauf Aregbesola.
A wata takarda da hadimin Aregbesola na yada labarai, Soka Fasure ya fitar, ya ce rahoton da ake yaduwa a yanar gizo ya saba dokokin jaridanci, The Nation ta wallafa.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sako 'yan makarantar Kagara, amma akwai wasu kalubale
Kamar yadda takardar tace, marubucin ya yi ikirarin karya na cewa ministan cikin gida kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola, wurin karshen mulkinsa ya samu dukkan albashinsa a sirrance, akasin yadda yayi ikirari.
"Rahoton dukkan shi labarin kanzon kurege ne, labarin bogi kuma mara amfani a jaridance."
Hadimin ya ce: "Bari in sake bayyanawa, Ogbeni Aregbesola bai taba karbar albashi ba a shugabancin jihar Osun da yayi na shekaru takwas.
"Dalilansa sune gwamnati ta samar da wurin zama, tsaro, sufuri, abinci da sauran ababen amfanin rayuwa. Don haka babu bukatar a biya shi wasu kudade.
"Ya kara da yin bayanin cewa dukkan 'ya'yansa sun girma kuma sun kammala karatu don haka babu bukatar biya musu kudin makaranta. A don haka ya sadaukar da albashinsa ga gwamnatin jihar.
"Marubucin rahoton ya yi ikirarin cewa ya samu bayanan ne daga wasu jami'an gwamnati amma ba a samar da shaida ba."
KU KARANTA: Caccakar Buhari: DSS ta cafke hadimin Ganduje, Dawisu, bayan yace APC ta gaza
A wani labari na daban, a wani lamari mai taba zuciya a Najeriya, wasu 'yan bindiga sun bindige wasu mutane 22 a jihar Zamfara.
A ranar Alhamis, 25 ga watan Fabrairun 2021, 'yan bindiga sun kai samame inda suka kashe a kalla mtum 22, Daily Trust ta wallafa.
Kamar yadda aka gani, lamarin ya faru a wani wurin hakar zinari da ke kusa da Sabuwar Tunga a kauyen Dankurmi da ke karamar hukumar Maru.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng