Mayakan ISWAP sun kaiwa kwamandan Operation Lafiya Dole farmaki a Borno

Mayakan ISWAP sun kaiwa kwamandan Operation Lafiya Dole farmaki a Borno

- Mayakan ta'addanci na ISWAP sun kaiwa kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole hari

- Kamar yadda aka gano, sun kai farmakin ne a kauyen Garin Kuturu da ke tsakiyar Auno da Jakana

- Duk da ba a san yawan 'yan ta'addan da aka kashe ba, an halaka sojoji biyu a musayar wutan

A ranar Lahadi, mayakan ta'addanci na ISWAP sun kaiwa wani babban kwamandan sojojin Najeriya, Farouq Yahaya farmaki.

Farouq Yahaya, soja mai mukamin Manjo Janar, ya zama kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole a watan Afirilun 2020 bayan saukar Manjo Janar Olusegun Adeniyi.

HumAngle ta gano cewa mayakan ISWAP sun kai masa harin ne a kauyen garin Kuturu da ke tsakanin Auno da Jakana kusa da babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

KU KARANTA: Kagara: 'Yan bindiga basu tausayi ko tsoro, sun ce alkawarinsu gwamnati ta karya, Hauwa

Mayakan ISWAP sun kaiwa kwamandan Operation Lafiya Dole farmaki a Borno
Mayakan ISWAP sun kaiwa kwamandan Operation Lafiya Dole farmaki a Borno. Hoto daga @HumAngle
Source: Twitter

A kalla sojoji biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon musayar ruwan wutar da aka yi tsakanin sojin Najeriya da 'yan ta'addan.

Duk da 'yan ta'addan sun karar da motar yaki guda daya, HumAngle bata tabbatar da yawan 'yan ta'addan da aka kashe ba.

A ranar 6 ga watan Janairun 2020, 'yan ta'addan sun kai wa tsohon kwamandan Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi farmaki.

Babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu ta zama hanya mai cike da hatsari ga farar hula da jami'an tsaro.

KU KARANTA: Caccakar Buhari: DSS ta cafke hadimin Ganduje, Dawisu, bayan yace APC ta gaza

A wani labari na daban, dalibai tare da malaman kwalejin kimiyya ta Kagara da ke jihar Neja sun isa babban birnin jihar, Minna.

Dalibai 27, malamai 3 tare da wasu mutum 12 ne aka sace yayin harin da aka kai makarantar. A wani bidiyo, an ga daliban suna fitowa daga dajin. An gano cewa an nadi bidiyon a wurin makarantar sakandare na Attahiru da ke Madaka a jihar Neja.

Jibrin Usman, kakakin ma'aikatar ilimi ta jihar Neja ya ce an tuntubi kwamishinan ilimi na jihar domin ya karba yaran kafin su gana da gwamnan jihar.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel