Yanzu-yanzu: Majalisa ta shiga zaman tantance sabon shugaban EFCC, Rasheed Bawa a yau

Yanzu-yanzu: Majalisa ta shiga zaman tantance sabon shugaban EFCC, Rasheed Bawa a yau

- Biyo bayan nadin da shugaba Buhari yayi wa Abdurrasheed Bawa, yau za a tantace shi

- Majalisar Dattawa ta shuga zaman tantace jami'in a yau domin kama aikin matsayinsa

- Ana sa ran zai karbi kujerar da Magu ya bari a shekarar 2020 biyo bayan wata badakala

Majalisar dattijai ta fara tantance sabon Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, Vanguard ta ruwaito.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Babajide Omoworare ne ya gabatar da Bawa wanda tuni ya kasance a dakin taron.

KU KARANTA: Babu wanda ya mallaki AK-47 a cikinmu, Manoma sun caccaki gwamna Lalong

Yanzu-yanzu: Majalisa ta shiga zaman tantance sabon shugaban EFCC, Rasheed Bawa a yau
Yanzu-yanzu: Majalisa ta shiga zaman tantance sabon shugaban EFCC, Rasheed Bawa a yau Hoto: Legit.ng
Asali: Twitter

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya yi alkawarin cewa Sanatoci kowa na iya yin duk tambayar da zai yi, kamar dai yadda ya ce tantancewar za ta ba da dama ga Shugaban Hukumar yaki da rashawa.

Ka tuna cewa Lawan ya fada a makon da ya gabata cewa za a tantance Abdurrasheed Bawa a zauren majalisa

Bayan tabbatarwar Majalisar Dattawa, ana sa ran Bawa zai karbi mulki daga hannun Mohammed Umar Abba da Shugaba Buhari ya nada a matsayin Shugaban rikon kwarya bayan dakatar da tsohon Shugaban Hukumar EFCC na gaba, Ibrahim Magu.

KU KARANTA: Najeriya da sauran kasashe 9 masu yawan mutane da basu da wutan lantarki

A wani labarin, Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Misis Amina Mohammed ta roki Gwamnatin Tarayya ta kara sanya jari a kan matasa a matsayin wata hanya ta magance rashin tsaro, a rahoton Channels Tv.

Da take magana yayin ziyarar girmamawa ga Ministan Harkokin Wajen Najeriya Mista Geoffrey Onyeama, Misis Amina ta lura cewa ya kamata a bai wa matasa da sauran ‘yan Nijeriya wani abin da za su sa ido domin bayar da gudummawa ga ci gaban kasar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.