An yi na ƙarshe: Buhari ya bawa ƴan Nigeria tabbacin ba za a sake satar ɗalibai ba bayan na Jangeɓe

An yi na ƙarshe: Buhari ya bawa ƴan Nigeria tabbacin ba za a sake satar ɗalibai ba bayan na Jangeɓe

- Shugaba Muhammadu Buhari ya bawa ƴan Nigeria tabbacin ba za a sake sace ɗalibai ba bayan na Jangeɓe

- Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ta bakin Ministan Sufurin Jiragen sama, Hadi Sirika a ranar Lahadi yayin ziyarar jaje a Zamfara

- Shugaban ƙasar ya ce gwamnatin tarayya ta ɗauki sabbin matakin ganin bai sake faruwa ba a kasar

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a, ya bawa ƴan Najeriya tabbacin wannan shine karo na ƙarshe da ƴan bindiga za su sace ɗalibai a makaranta kamar yadda ta faru a Jangebe, Zamfara, Daily Trust ta ruwaito.

Sanarwar ta shugaban ta fito a ranar Lahadi ne ta bakin Ministan Sufurin Jiragen sama, Hadi Sirika, wanda ya jagoranci wata babban tawagar zuwa Zamfara don jaje ga jama'a kan sace yaran.

An yi na ƙarshe: Buhari ya bawa ƴan Nigeria tabbacin ba za a sake satar ɗalibai ba bayan na Jangeɓe
An yi na ƙarshe: Buhari ya bawa ƴan Nigeria tabbacin ba za a sake satar ɗalibai ba bayan na Jangeɓe. Hoto: @daily_tust
Asali: Twitter

Ya ce gwamnatin tarayya ta dauki sabbin matakai domin kawo karshen dukkan ayyukan ɓata gari a kasar.

DUBA WANNAN: Mutum 9 sun mutu, 41 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Kano

"Shugaban ƙasa ya yi bakin cikin sace ɗalibai daga Jangebe sannan yana baku tabbacin gwamnati na da dukkan abinda ake bukata don maganin ɓata garin," in ji shi.

Buhari ya kuma yabawa Gwamna Bello Matawalle na Zamfara bisa ƙokarinsa na kawo karshen ƴan bindigan yana mai alƙawarin cigaba da bashi goyon bayan don samun zaman lafiya mai dorewa.

"Gwamnatin tarayya za ta cigaba da hadin gwiwa da gwamnatin Zamfara da jama'ar jihar a ƙoƙarin ta na magance ƙallubalen rashin tsaro a jihar," in ji Buhari.

A bangarensa, Gwamna Bello Matawalle ya yi wa Shugaba Buhari da gwamnatin tarayya godiya, inda ya ce nan bada daɗewa ba za a sako waɗanda aka yi garkuwa da su.

"Na yi imani da shugaba kasa da ƙokarinsa na yaki da dukkan masu laifuka domin inganta tsaro a kasar.

"Hakan zai yiwu ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro domin a tunkari ɓata garin a kasa da sama a lokaci guda," in ji gwamnan.

KU KARANTA: Tsaro: 'Yan bindiga sun kashe mutane bakwai a jihar Kaduna

Sauran mambobin tawagar sun hada da Ministan Harkokin Ƴan sanda, Alhaji Mai gari Dingyaɗi, Ministan Harkokin Jin Ƙai, Hajiya Sadiya Umar Farouk da ministan harkokin mata, Mrs Pauline Tallen.

Fiye da ɗalibai 300 ne aka sace daga Makarantar Mata ta Gwamnati da ke Jangebe, Talata Mafara a jihar Zamfara da ƴan bindiga suka kai hari a ranar Juma'a kamar yadda NAN ta ruwaito.

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel