'Yan sanda sun kame 'yan fashi 40 a babban birnin tarayya Abuja

'Yan sanda sun kame 'yan fashi 40 a babban birnin tarayya Abuja

- Rundunar 'yan sanda sun samu nasarar cafke wasu 'yan fashi a wani yankin babban birnin Abuja

- Sun kama akalla mutane 40 da ake zargin 'yan fashi ne yayin da aka gurfanar dasu gaban a kotu

- Rundunar 'yan sandan ta bada lambobin waya domin tuntubarsu kan lamarin batanci a yankin

Rundunar ‘yan sanda ta Abuja ta kama mutum arba’in da ake zargi da laifin satar mota, fataucin muggan kwayoyi, fashi da makami da sauran laifuka a yankunan Abaji, Gwarinpa, Asokoro, Jabi-Daki biyu da Mabushi.

An kama wadanda ake zargin a yayin kai samame da sintiri tsakanin ranakun 18 zuwa 24 ga Fabrairu, 2021, Vanguard News ta ruwaito.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar ta Abuja, ASP Yusuf Mariam ya lissafa wadanda ake zargin kamar haka: Tijani Zariwa dan shekara 25, Shamsudeen Abdullahi dan shekara 20, Muktari Mohammed dan shekara 48, Yahaya Abdullahi dan shekara20, Abbas Mohammed dan shekara 24.

Hakazalika da Suleiman Audu dan shekara 19, Abubakar Baba dan shekara 34, Hudu Garba dan shekara 24, Sadiq Isa dan shekara 20, Yusuf Ali dan shekara 18, Abu Momoh Samuel da Simon Ndagi 'yan shekaru 34years duka maza da mace daya; Nwanse Precious yar shekara 22 da sauransu.

KU KARANTA: Tsohon Daraktan DSS: Da yawan 'yan bindiga tsofaffin 'yan Boko Haram ne

'Yan sanda sun kame 'yan fashi 40 a babban birnin tarayya Abuja
'Yan sanda sun kame 'yan fashi 40 a babban birnin tarayya Abuja Hoto: Premium Times Nigeria
Asali: UGC

Yusuf ya ce kayayyakin da aka samu a wurin wadanda ake zargin sun hada da: Farar Toyota Hilux guda daya, Toyota Corolla daya, bindiga kirar gida guda daya da harsasai 21 da ba a yi amfani dasu ba.

“Daga cikin wadanda ake zargin sun hada da Olamide Atanda dan shekara 29, da Osas Raphel mai shekara 32, wadanda aka kamasu saboda kwace mota bayan sun kai hari tare da tattaka wanda suka yi wa satan a hanyar Lugbe.

"Jami'an 'yan sanda masu sa ido sun gano motar a yayin aikin bincike a kan hanyar Abaji. An kuma kwace: Toyota Corolla mai launin toka guda daya."

An gurfanar da dukkan wadanda ake zargin a gaban kotu in banda 'yan fashin motar, za a gurfanar da su gabanin kammala bincike.

“Muna umartar mazauna yankin da su kasance masu natsuwa, masu bin doka da kuma bin duk dokokin COVID-19.

“A yanzu haka rundunar tana son sake jaddada kudirin ta na kare rayuka da dukiyoyi a cikin babban birnin tarayya.

"Rundunar tana kirayi mazauna yankin da su kokarta wajen kai rahoton duk wani motsin da ba su yarda da shi ba." In ji PRO.

Hakazalika rundunar 'yan sandan ta bada lamobin waya kamar haka: 08032003913, 08061581938, 07057337653 da 08028940883. Hakazalika za a iya kiran layin Ofishin Karar Jama'a (PCB): 09022222352, domin tuntuba cikin gaggawa.

KU KARANTA: Soyinka: Ya kamata duk jihar da ake sace yara su tsunduma zanga-zanga

A wani labarin, Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) a jiya ta yi kira ga iyayen da ke da ’ya’ya a makarantun kwana a yankin arewa cewa kada su karaya game da yawan sace-sacen mutane ba kakkautawa a jihohin Zamfara da Neja, Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar, ta bakin Daraktan Yada Labarai da Bayar da Shawara, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya kuma nuna kaduwa da haushi game da yawaitar sace-sacen yara ‘yan makarantar kwana a sassa daban-daban na Arewa.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel