Rana bata karya: Ganduje ya saka ranar mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano
- Gwamnatin jihar Kano ta saka ranar yin mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da malaman jihar
- Za a yi wannan mukabala ne a ranar Lahadi, 7 ga watan Maris kamar yadda kwmaishinan labarai da na harkokin addini suka tabbatar
- An shirya muhawarar ne domin a samu fahimtar juna tsakanin wadannan bangarori
Labari da muke samu a yanzu shine cewa gwamnatin jihar Kano ta sanya ranar Lahadi, 7 ga watan Maris, a matsayin ranar yin mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da kuma malaman jihar.
Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa kwamishinan Yada Labaran Kano, Muhammad Garba da kuma takwaransa na Ma’aikatar Harkokin Addini, Dokta Muhammad Tahir, sun tabbatar da hakan.
KU KARANTA KUMA: Iyayen daliban Zamfara sun bayyana tsoron da suke ji a kan 'ya'yansu
Kwanaki Legit.ng ta kawo cewa za a zauna ayi baja-kolin hujjoji da dalilan addini tsakanin Abduljabar Nasiru Kabara da sauran manyan Malaman Kano na Ahlul-Sunnah.
Abdullahi Ganduje ya shirya taron muhawara a tsakanin Abduljabbar Nasiru Kabara, da sauran Malamai domin a samu fahimtar juna tsakanin wadannan bangarori.
Hakan na zuwa ne bayan an yi ta neman gwamnati ta yi na'am da zaman mukabala irin haka.
A gefe guda kuma, babban malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya tofa albarkacin bakinsa game da sabanin da aka samu da Abduljabbar Nasiru Kabara.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya fito ya yi kira ga gwamnatin Kano da malaman Ahul-Sunnah da su guji yin mukabala da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
KU KARANTA KUMA: Dattawan Arewa ga 'yan Arewa: Dan Allah kada ku debe 'ya'yan ku a makarantun kwana
Shehin malamin ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da wani karatun fiqihu a garin Kaduna.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng