Iyayen daliban Zamfara sun bayyana tsoron da suke ji a kan 'ya'yansu

Iyayen daliban Zamfara sun bayyana tsoron da suke ji a kan 'ya'yansu

- Da yawa daga cikin iyayen yan matan da yan bindiga suka sace a makarantar GGSS Jangebe, jihar Zamfara sun bayyana babban damuwarsu

- Sun nuna damuwarsu kan yiwuwar azabtar da ’ya’yan nasu da yunwa da matsanancin sanyi, da nauo’in cin zarafi da zai dade yana damun su

- Har ila yau sun damu a kan halin da yaran za su kasance ta fannin lafiyarsu ko bayan sakinsu

Iyayen ‘yan mata sama da 300 da aka sace daga wata makarantar Zamfara kwanakin baya sun nuna damuwar su game da yiwuwar‘ ya’yansu mata na fuskantar matsanancin yunwa, yin lalata da su, tsananin sanyi da rashin lafiya.

Yawancin iyayen da suka zanta da jaridar Daily Trust a ranar Asabar sun kuma ce sun damu matuka don ana iya ajiye yaransu a cikin mawuyacin yanayi; saboda haka suna iya kamuwa da rashin lafiyar da ka iya cutar da su, koda bayan sun sami 'yanci.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai hari garuruwa uku a Neja cikin sa’o’i biyu, sun kashe 3 da yin garkuwa da wasu da dama

Iyayen daliban Zamfara sun damu da halin da suke ciki ta fuskacin yunwa da tsaron martabobinsu ta ‘ya’ya mata
Iyayen daliban Zamfara sun damu da halin da suke ciki ta fuskacin yunwa da tsaron martabobinsu ta ‘ya’ya mata Hoto: Daily Trust
Source: UGC

Sadiya Kawaye, wacce aka sace ‘ya’yanta mata biyu, ta ce, "Saboda yawan daliban da aka sace, mun yi imanin cewa za su shiga cikin mummunan hali na dimuwa.

“‘Yan bindigan ba za su iya ciyar da dalibai masu yawa haka da kyau ba. A ina zasu samo abincin da zasu basu? Har ila yau, muna damuwa game da cin zarafi na lalata da za su iya fuskanta a can.

“An kwashe wadannan‘ yan matan ne yayin da suke bacci. Mun ji cewa wasu daga cikinsu, saboda tsoro ko tashin hankali, ba su iya ɗaukar abun lullubarsu ko barguna ba.''

Wani mahaifin daya daga cikin daliban, wanda ya bayyana kansa a matsayin Ibrahim, ya ce ‘yarsa tana shan magani, kuma ya nuna damuwarsa kan cewa halin da take ciki zai iya munana.

“Daf da komawarta makaranta, mun dauke ta zuwa asibiti, inda aka duba ta sannan aka daura ta a kan magunguna. Ta yaya zata murmure yayin da yunwa da sanyi ka iya addabe ta?

KU KARANTA KUMA: Dattawan Arewa ga 'yan Arewa: Dan Allah kada ku debe 'ya'yan ku a makarantun kwana

“Mun ga yadda daliban makarantar Kankara suka fita daga hayyacinsu yayin da aka sake su, galibi saboda yunwa. Wahalar da za su sha ta fi karfinsu,” inji shi.

A wani labarin, wasu daga cikin daliban sakandiren gwamnati ta Jangebe da ke jihar Zamfara da suka tsira, sun ce har da mata a cikin gungun ’yan bindigar da suka kai musu hari.

A ranar Juma’a ne yan bindiga suka kai mamaya makarantar wacce ke a karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar.

An tattaro cewa 'yan bindigar sun isa makarantar ne da sanyin safiyar ranar Juma'a, inda suka sace dalibai yan tsakanin shekaru 12 zuwa 16 daga dakunansu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel