Sheikh Gumi ya ba Ganduje da Malaman Kano shawarwari 3 a kan zama da Abduljabbar

Sheikh Gumi ya ba Ganduje da Malaman Kano shawarwari 3 a kan zama da Abduljabbar

- Ahmad Mahmud Gumi ba ya goyon bayan a zauna da Abduljabbar Kabara

- Sheikh Gumi ya ce Abduljabbar Nasiru Kabara ya na kan tafarkin Shi’a ne

- A dalilin haka Malamin yake ganin kan bangarorin malaman ba zai hadu ba

Babban malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya tofa albarkacin bakinsa game da sabanin da aka samu da Abduljabbar Nasiru Kabara.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya fito ya yi kira ga gwamnatin Kano da malaman Ahul-Sunnah da su guji yin mukabala da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Shehin malamin ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da wani karatun fiqihu a garin Kaduna.

A wannan bidiyo da ya shigo hannunmu, malamin ya bada shawarwari uku da yake ganin za su yi wa gwamnatin Dr. Abdullahi Ganduje da malaman jihar Kano amfani.

KU KARANTA: Sanusi II ya yi magana a kan sabanin Abduljabbar da malaman addini

Ahmad Abubakar Gumi ya jefi Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da rigar shi’a, ya ce don haka ba za a taba samun matsaya tsakaninsa da sauran malaman Kano ba.

A ra’ayin Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ba za a iya cin ma madogararar da za a tattauna a kai, tsakanin masu da’awar Ahlul-Sunnah, da malamin da ke bin shi’a ba.

Gumi ya bayyana cewa a karshen wannan zama, sauran gama-garin al’umma ba za su iya gane mai gaskiya tsakanin Abduljabbar Kabara da ragowar malaman ba.

Shehin ya yabi mahaifin wannan malami, Sheikh Nasiru Kabara, wanda a cewarsa ya zo har masallacin Sultan Bello, ya yaba da koyarwar Marigayi Ahmad Gumi.

KU KARANTA: MURIC ba ta goyon bayan a zauna da Abduljabbar Kabara

Sheikh Gumi ya ba Ganduje da Malaman Kano shawarwari 3 a kan zama da Abduljabbar
Sheikh Ahmad Gumi Hoto: www.dailytrust.com
Source: UGC

Ahmad Gumi ya bayyana cewa akwai abin da Abduljabbar Nasiru Kabara yake nufi a zuciyarsa, ya yi masa addu’a, kuma ya bada shawarar rufe taba hadisan Annabi.

Kwanaki kun ji cewa za a zauna ayi baja-kolin hujjoji da dalilan addini tsakanin Abduljabar Nasiru Kabara da sauran manyan Malaman Kano na Ahlul-Sunnah.

Abdullahi Ganduje ya shirya taron muhawara a tsakanin Abduljabbar Nasiru Kabara, da sauran Malamai domin a samu fahimtar juna tsakanin wadannan bangarori.

Hakan na zuwa ne bayan an yi ta neman gwamnati ta yi na'am da zaman mukabala irin haka.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel