Ganduje ya shirya muhawara tsakanin Abduljabar da manyan Malaman Kano

Ganduje ya shirya muhawara tsakanin Abduljabar da manyan Malaman Kano

_ Za'a yi zubeben kwarya a kuma bajeta a faifai a tsakanin Abduljabar Nasiru Kabara da sauran manyan Malaman Kano

- Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar, Ganduje ya amince da hakan bayan manyan Malamai sun shawarce shi

- An bawa kowanne bangare tsawon sati biyu domin yin shirin muhawarar; wacce za'a watsa kai tsaye a kafafen yada labarai na gida da ketare

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ya shirya taron muhawara a tsakanin Malamin Islama, Abduljabbar Nasiru Kabara, da sauran manyan Malamai daga sauran dariku domin a bajeta a faifai.

A ranar Juma'a ne gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwar dakatar da Abduljabar daga gudanar da wa'azi tare da rufe Masallacinsa.

Sai dai, rahotanni sun wallafa cewa a wani yunkuri na warware sabanin fahimta da ke tsakanin Abduljabar da sauran Malaman dariku, gwama Ganduje ya sanar da cewa za'a gudanar da muhawara.

"Gwamna Ganduje ya amince da bukatar a gudanar da muhawara domin ware duk wani sabanin fahimta da ke tsakanin Abduljabar da sauran Malamai.

KARANTA: Duban kurilla: 'Yan Nigeria sun hango kurakurai biyu a jikin sabon katin APC na Tinubu

Ganduje ya shirya muhawara tsakanin Abduljabar da manyan Malaman Kano
Ganduje ya shirya muhawara tsakanin Abduljabar da manyan Malaman Kano @Freedomradio
Asali: Twitter

"Hakan ya biyo bayan tattaunawar da ta gudana tsakanin gwamna Ganduje da sauran manyan Malamai daga sauran dariku da kuma jami'an gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkokin addinin Musulunci," kamar yadda Abba Anwar, kakakin gwamna Ganduje, ya fitar da sanarwa.

Wakilan gwamnati da suka halarci taron sun hada da kwamishinan harkokin addini, Tahar Adamu da shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Ali Makoda.

Tsohon dan takarar gwamna, Salihu Sagir Takai, da sauran manyan Malaman addini duk sun halarci taron.

KARANTA: Mamaki: APGA ta kayar da manyan jam'iyyu a zaben maye gurbin wakilin mazabar Magama/Rijau

Sanarwar Anwar, wacce ta fito bayan kammala taron, ta cigaba da cewa; "dukkan manyan Malamai zasu halarci wurin taron muhawarar, sannan za'a gayyato manyan Malamai daga wajen jihar Kano.

"Gwamna Ganduje ya amince da hakan kuma ya dauki alhakin samar da wurin da za'a yi taron muhawarar.

"Dukkan wadanda zasu fafata daga kowanne bangare an basu sati biyu domin su shirya.

"Kazalika gwamna Ganduje ya amince cewa za'a yada muhawarar kai tsaye a gidajen radiyo na gida da ketare.

"Gwamna Ganduje ya na kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu hakuri kafin da kuma yayin gudanar da muhawarar da kuma har ma bayan kammala ta baki daya," a cewar Anwar.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Cif John Odigie-Oyegun, tsohon shugaban jam'iyyar APC, ya ki amincewa da ra'ayin Tinubu da Akande akan sabunta rijista.

Dattijo a APC, Bisi Akande, ya soki aikin sabunta rijistar mambobin jam'iyyar da shugabanci riko a karkashin Mai Mala Buni ke cigaba da gudanarwa.

A yayin da ya ke karbar sabuwar rijitarsa a ranar Asabar, Tinubu ya bayyana cewa yana goyon bayan ra'ayin Akande akan cewa babu bukatar aikin sake sabunta rijistar mambobi.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.googlecom/stor.e/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel