Babban magana: Akwai mata cikin yan bindigar da suka sace daliban GGSS a Zamfara
- Daga cikin daliban da suka tsallake rijiya da baya a garkuwan da yan bindiga suka yi da daliban GGSS Jangebe sun ce akwai mata a cikin yan ta'addan
- Wata mai suna Madina Hamisu, ta ce tana tsaka da sharar bacci wata mata rike da bindiga ta tashe ta
- A ranar Juma’a ne yan bindiga suka kai hari makarantar wacce ke a karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar Zamfara tare da sace dalibai 317
Wasu daga cikin daliban sakandiren gwamnati ta Jangebe da ke jihar Zamfara da suka tsira, sun ce har da mata a cikin gungun ’yan bindigar da suka kai musu hari.
A ranar Juma’a ne yan bindiga suka kai mamaya makarantar wacce ke a karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar.
An tattaro cewa 'yan bindigar sun isa makarantar ne da sanyin safiyar ranar Juma'a, inda suka sace dalibai yan tsakanin shekaru 12 zuwa 16 daga dakunansu.
KU KARANTA KUMA: Sallamar Salihu Tanko Yakasai daga matsayin hadimin Ganduje ya janyo cece-kuce
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Madina Hamisu Kawaye, daya daga cikin daliban da ta kubuta a lamarin, ta ba da labarin abin da ya faru.
“Wata mata sanye da bakakken tufafi ta tashe ni ta hanyar buga bindiga a kan gadona sannan ta daka min tsawa. Na farka cikin tsoro. Na lura cewa ana fitar da abokan karatuna da yawa daga ɗakin kwanan mu.
"Wasu daga cikinsu sun rufe jikinsu da bargunansu," in ji dalibar.
Kawaye ta ce ta labe ne a yayin da matar mai dauke da makami ta je tayar da sauran dalibai daga barci. Ta labe a karkashin gadon tare da wasu daliban biyu.
“Suna tambayar kudi da wayoyi. Daya daga cikin matan ta tambayi inda mai kula da dalibai take.
"Na ji wani daga cikin 'yan bindigar yana fadawa wani a waya cewa sun shigo makarantar kuma cewa sun fara tattara dalibai da yawa," in ji ta.
Ta ce daya daga cikin ‘yan bindigar ya yi magana a cikin harshen Fulfulde, inda ta kara da cewa “hakika wannan lokaci ne mai matukar wahala a gare mu. Ba mu iya fita daga inda muka buya ba har sai da suka bar dakunan kwanan.”
Wata da ta tsallake rijiya da baya wacce ta bayyana sunanta a matsayin Zainab, ta ce ta tsere zuwa cikin bandaki a lokacin da aka tattara su a kusa da masallacin makarantar, ana shirin kai su cikin motocin.
Ta ce, “Na fice daga cikin mutanen da gudu na shige cikin bandaki.
“Daga inda na buya a cikin bandakin, na ji karar harbe-harbe yayin da motocinsu suka fice zuwa cikin dajin. Muna ta kuka muna rokon su da su yi mana rai.”
Wani uba a garin Kawaye da ke karamar Hukumar Anka, Malam Sadi Kawaye, ya ce wasu ‘ya’yansa mata biyu, Mansura da Sakina, suna daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya cika da farin ciki yayinda aka saki daliban makarantar Kagara
“Na samu labarin sace yaran ne da misalin karfe 3 na dare kuma nan da nan bayan Sallar Subhi, sai na tafi yankin da makarantar take sannan na dawo tare da‘ yan mata biyar daga yankinmu da suka yi nasarar tserewa. Tara suna tare da masu garkuwan," in ji shi.
A wani labarin, mun ji cewa domin samun nasaran ceto dalibai mata 317 da aka sace ranar Juma'a, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya nemi taimakon tubabbun dan bindiga Auwalu Daudawa da Zakoa Buhari, ThisDay ta ruwaito.
Auwalu Daudawa ne dan bindigan da ya jagoranci satan daliban makarantan sakandaren GCSS, Kankara, a jihar Katsina.
Zakoa Buhari kuma shine dan shahrarren kasurgumin dan bindiga, Buhari Daji.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng