Buhari ya cika da farin ciki yayinda aka saki daliban makarantar Kagara

Buhari ya cika da farin ciki yayinda aka saki daliban makarantar Kagara

- Shugaba Buhari ya nuna farin ciki da jin dadi a kan sakin daliban makarantar gwamnati ta Kagara, jihar Neja

- Buhari ya yaba ma hukumomin tsaro da gwamnatin Neja a kan namijin kokarin da suka yi wajen ceto yaran

- Ya kuma yi kira ga masu makarantu a kan su tsaurara tsaro a makarantunsu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi maraba da sakin daliban da aka sace na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara, Jihar Neja, Nigerian Tribune ta ruwaito.

A wata sanarwa da Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban Kasa a kafofin watsa labarai ya fitar a ranar Asabar, ya ce Shugaban kasar ya yaba wa hukumomin tsaro da na leken asiri kasae da kuma gwamnatin jihar Neja kan martaninsu wajen ceto yaran.

Sanarwar ta ruwaito Buhari yana cewa: "Muna farin ciki da sakin su" in ji Shugaba Buhari, wanda ya kuma tausaya ma ma'aikatan da daliban, iyayensu da abokansu kan wannan jarabawar.

Buhari ya cika da farin ciki yayinda aka saki daliban makarantar Kagara
Buhari ya cika da farin ciki yayinda aka saki daliban makarantar Kagara Hoto: Naijaloaded
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: Yan ta’addan Boko Haram sun saki amaryar da aka sace a Borno

Ya kuma yi gargadin cewa kasar ba za ta ci gaba da fuskantar wadannan hare-hare da ke barazana ga ci gaban ilimi, tsaro da rayuwar shugabannin da za su zo nan gaba ba da kuma jefa al’ummar kasar cikin mummunan yanayi.

Shugaban ya jaddada shawarar da ya ba masu makarantu tun farko, musamman na gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da kungiyoyin addinai da su kara tsaro a makarantunsu daidai da ka'idojin shirin tsaron makarantu na Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaba Buhari ya sake yin tir da Allah wadai game da sace daliban, inda na baya-bayan nan ya kasance a makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe a jihar Zamfara.

Sannan ya umarci dukkanin jami'an tsaro da jami'an leken asirin kasar da su yi farautar masu laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

KU KARANTA KUMA: Tanko Yakasai ya tabbatar da cewar jami’an tsaro sun kama dansa hadimin Ganduje

A baya mun ji cewa 'yan bindiga sun saki 'yan makarantar kwalejin kimiyya ta gwamnati tare da malamansu da aka sace.

An sako su a sa'o'in farko na ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairun 2021, jaridar Vanguard ta wallafa.

Majiya mai karfi ta sanar da cewa a halin yanzu wadanda aka sace suna kan hanyarsu ta zuwa Minna kuma nan da sa'o'i kadan za su isa babban birnin.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel