Satar ‘yan matan Zamfara: Buhari gargadi gwamnoni kan saka wa 'yan fashi da kyautar kudi

Satar ‘yan matan Zamfara: Buhari gargadi gwamnoni kan saka wa 'yan fashi da kyautar kudi

- Shugaba Buhari ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a ceto yaran makarantar da aka sace

- Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a ranar Juma’a, 26 ga watan Fabrairu, sun kai mamaya wata makarantar sakandaren ‘yan mata ta gwamnati, Zamfara sannan suka sace ‘yan mata 317.

- Sai dai kuma, Buhari ya shawarci gwamnoni da kada su saka wa ‘yan fashi kan ayyukansu da baya bisa ka’ida

An gargaɗi gwamnonin kasar da su daina saka wa 'yan fashi da kudi da kuma motoci domin kaucewa mummunan sakamako.

Jaridar Nigeria Tribune ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bada wannan gargadin a ranar Juma’a, 26 ga watan Fabrairu, inda ya ce al’adar biyan wasu bata gari da wasu gwamnatocin jihohi ke yi na iya haifar da ‘da mara ido.

KU KARANTA KUMA: Tanko Yakasai ya tabbatar da cewar jami’an tsaro sun kama dansa hadimin Ganduje

Yan matan Zamfara: Buhari ya gargadi gwamnoni a kan saka wa 'yan fashi da kyautar kudi
Yan matan Zamfara: Buhari ya gargadi gwamnoni a kan saka wa 'yan fashi da kyautar kudi Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake maida martani kan sace daruruwan daliban Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Gwamnati, Jangebe a jihar Zamfara, yana mai lura da cewa satar rashin imani ne kuma sam ba za a yarda da ita ba.

Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannunsa, ya bayyana cewa Buhari ya ce babu wata kungiyar masu laifi da za ta fi karfin gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: Yan ta’addan Boko Haram sun saki amaryar da aka sace a Borno

Ya ce abin da kawai ke tsayawa tsakanin jami'an tsaro da 'yan fashi su ne ka'idojin aiki.

Shugaban ya kuma shawarci jihohi da kananan hukumomi da su kara kaimi ta hanyar inganta tsaro a makarantu da kewayen su.

"Rikicin garkuwa da mutane wani abu ne mai sarkakiya wanda ke bukatar cikakken hakuri domin kare wadanda abin ya shafa daga cutarwa ta jiki ko ma mummunan kisa a hannun wadanda suka yi garkuwa da su."

A wani labarin, 'yan bindiga sun saki 'yan makarantar kwalejin kimiyya ta gwamnati tare da malamansu da aka sace.

An sako su a sa'o'in farko na ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairun 2021, jaridar Vanguard ta wallafa.

Majiya mai karfi ta sanar da cewa a halin yanzu wadanda aka sace suna kan hanyarsu ta zuwa Minna kuma nan da sa'o'i kadan za su isa babban birnin.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng