Tanko Yakasai ya tabbatar da cewar jami’an tsaro sun kama dansa hadimin Ganduje

Tanko Yakasai ya tabbatar da cewar jami’an tsaro sun kama dansa hadimin Ganduje

- Jigon Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya tabbatar da cewar jami'an tsaro sun kama dansa kuma hadimin gwamna Ganduje, Salihu

- Sai dai bai bayyana takamaiman hukumar tsaron da ta tsare dan nasa ba

- Yakasai ya ce Salihu na a hanyarsa ta dawowa daga wajen aski a ranar Juma'a lokacin da jami'an tsaron suka damke shi

Alhaji Tanko Yakasai, jigo a kungiyar dattawan Arewa kuma uba ga mai taimaka wa Ganduje kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya tabbatar da cewa dansa (Salihu) yana tsare a hannun jami’an tsaro.

Kodayake, bai bayyana takamaiman hukumar tsaron da ta tsare dan nasa ba.

KU KARANTA KUMA: Ta tabbata: Ba sauran kaiwa kudu kayan abinci, tirelolin Albasa sun bar Nigeria

Tanko Yakasai ya tabbatar da cewar jami’an tsaro sun kama dansa hadimin Ganduje
Tanko Yakasai ya tabbatar da cewar jami’an tsaro sun kama dansa hadimin Ganduje Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Yakasai a wata hira ta wayar tarho da jaridar Vanguard a safiyar ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu, ya ce an tsare dan nasa ne tun daga ranar Juma’a lokacin da ya tafi gidan aski kuma yana kan hanyarsa ta komawa gida.

A cewarsa, “Yana hannun jami’an tsaro ba masu satar mutane ba. Ban san wanne daga cikin hukumar tsaron ba a yanzu saboda suna da suna da yawa.

“An dauke shi ne a jiya (Juma’a) lokacin da ya je aski lokacin da yake dawowa. Amma babu wani abin damuwa tunda yana tare da jami'an tsaro ba masu satar mutane ba," in ji Yakasai.

KU KARANTA KUMA: 2023: Jerin tsoffin gwamnoni shida da ke hararar kujerar shugabancin APC

Idan za ku tuna, a ranar Juma'a, 26 ga watan Fabrairu ne hadimin Gwamna Ganduje na jihar Kano, Salihu Yakasai, ya bukaci gwamnatin APC ta shawo kan ta'addanci ko kuma tayi murabus.

A wallafar da Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu yayi a shafinsa na Twitter bayan samun labarin satar 'yan matan daga makarantar Jangebe, ya bukaci gwamnatin APC da ta kawo karshen 'yan ta'adda ko tayi murabus.

"A bayyane yake a matsayinmu na gwamnatin APC mun gaza a kowanne mataki. Mun gaza ga 'yan Najeriya domin hakkinmu na farko bayan zabenmu shine baiwa rayuka da kadarori tsaro.

"Babu ranar da za ta fito ta fadi ba tare da an samu ire-iren haka ba a kasar nan. Wannan abun kunya ne. A yi maganin ta'addanci ko a yi murabus," ya wallafa.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel