Da duminsa: 'Yan bindiga sun sako 'yan makarantar Kagara, amma akwai wasu kalubale
- Labari da ke bayyana yanzu shine na sako wadanda aka yi garkuwa da su a makarantar sakandaren Kagara
- Amma kuma sakatariyar yada labarai ta jihar ta ce akwai wasu kalubale don haka bai kamata a fara murna ba
- An sako su a sa'o'in farko na ranar Asabar amma a yanzu suna kan hanyarsu ta zuwa Minna da ke Neja
Daga bisani 'yan bindiga sun saki 'yan makarantar kwalejin kimiyya ta gwamnati tare da malamansu da aka sace.
An sako su a sa'o'in farko na ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairun 2021, jaridar Vanguard ta wallafa.
Majiya mai karfi ta sanar da cewa a halin yanzu wadanda aka sace suna kan hanyarsu ta zuwa Minna kuma nan da sa'o'i kadan za su isa babban birnin.
KU KARANTA: Satar fasinjoji: Sojoji sun dakile Boko Haram a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri
Babbar sakatariyar yada labarai, Mary Nole-Berje, ta ce duk da ta samu labarin sako wadanda aka sace, har yanzu gwamnati bata sanar da ita ba.
A kokarin kiyayewa, ta ce: "Na ji labarin sako su amma gwamnati bata sanar da ni ba saboda akwai wasu kalubale."
"Idan sun iso Minna lafiya kalau kuma Gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello ya karbesu ne zamu yarda kuma mu fara murna," tace.
KU KARANTA: Hotunan miyagun makaman da Zikwi tare da yaransa 2 suka mika ga Matawalle
A wani labari na daban, hadimin Gwamna Ganduje na jihar Kano, Salihu Yakasai, ya bukaci gwamnatin APC ta shawo kan ta'addanci ko kuma tayi murabus.
A wallafar da Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu yayi a shafinsa na Twitter bayan samun labarin satar 'yan matan daga makarantar Jangebe, ya bukaci gwamnatin APC da ta kawo karshen 'yan ta'adda ko tayi murabus.
A yau Juma'a, 26 ga watan Fabrairu ne arewacin Najeriya ta tashi da mugun labarin sake kwashe wasu 'yan mata a makarantar kwana da ke Jangebe ta jihar Zamfara.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng