2023: Jerin tsoffin gwamnoni shida da ke hararar kujerar shugabancin APC

2023: Jerin tsoffin gwamnoni shida da ke hararar kujerar shugabancin APC

- Yayinda wa'adin mulkin Mai Mala Buni ke shirin karewa a matsayin shugaban APC na rikon kwarya, an fara tattauna batun wanda zai gaje shi

- A yanzu dai akwai wasu tsoffin gwamnoni shida da ake ganin suna hararar kujerar shugabancin jam'iyyar mai mulki ta kasa

- Daga cikinsu akwai Sanata Al-Makura, Yari, Kashim, Modu-Sheriff da sauransu

Akwai alamu da ke nuna cewa wasu tsoffin gwamnoni shida sun fara wani yunkuri a karkashin kasa da tuntuba don neman kujerar shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wa’adin mulkin Mai Mala Buni na rikon kwarya wanda aka kaddamar a ranar 25 ga Yuni, 2020, don gudanar da harkokin jam’iyyar, biyo bayan rusa Kwamitin NWC karkashin jagorancin Adams Oshiomhole, zai kare a watan Yunin 2021.

KU KARANTA KUMA: Ku gayyaci Gumi da Shekau kafin ku dame ni, Igboho ya magantu bayan dakile kamunsa

2023: Jerin tsoffin gwamnoni shida da ke sanya ido kan kujerar shugabancin APC
2023: Jerin tsoffin gwamnoni shida da ke sanya ido kan kujerar shugabancin APC Hoto: @mdgoje1
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa majiyoyin jam’iyyar da dama sun fadawa jaridar cewa jiga-jigan jam’iyyar shida daga arewa sun fara tattaunawa don neman kujerar shugabancin.

Ya ce dukkan su tsoffin gwamnoni ne wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen kafuwar jam'iyyar a shekarar 2013, sannan ta kara da cewa dukkan 'yan takarar har yanzu ba su bayyana kudirinsu na neman kujerar ba a hukumance.

Jaridar ta ce ban da shugaban da ke kan karagar mulki, wanda shi ne gwamna mai ci (Yobe), wasu mutum uku, Cif Bisi Akande, Cif John Odigie Oyegun, da Kwamared Adams Oshiomhole sun kasance tsoffin gwamnoni.

Ga sunayen tsoffin gwamnonin da ke neman zama shugaban APC na kasa:

1. Sanata Al-Makura

2. Danjuma Goje

3. George Akume

4. Abdulaziz Yari

KU KARANTA KUMA: Satar yan matan Zamfara: ‘Yan jarida tsun tsallake rijiya da baya

5. Sanata Kashim Shettima

6. Sanata Ali Modu Sheriff

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi yan bindiga da ke adabar al'umma a sassan kasar, inda ya ce gwamnatinsa za ta iya yin maganin su.

A cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya ce shugaban kasar ya nuna damuwarsa kan karuwar ayyukan bata gari.

Ya ce idan ba domin ana iya amfani da wadanda aka sace a matsayin garkuwa ba wanda zai haifar da salwatar rayyuka, da tuni jami'an tsaro sun gama da su.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel